Gaskiya ta bayyana: Yadda wani baturen farfesan lissafi ya musulunta bayan nazarin Al-qur'ani

Gaskiya ta bayyana: Yadda wani baturen farfesan lissafi ya musulunta bayan nazarin Al-qur'ani

Daya daga cikin manyan furofesoshin da ake ji da su a fannin ilimin boko na lissafi a wata jami'an jihar Kansas, kasar Amurka, mai suna Jeffery Lang ya karbi musulunci bayan wani dogon nazari da binciken da yayi a kan Al'qur'ani mai girma.

Kamar dai yadda muka samu, Jeffery ya tashi ne ba addini amma daga baya ya shiga addinin Kiristanci wanda yace ya kasa gamsar da shi cewa shine addinin gaskiya kafin daga bisani ya fita ya rungumi musulunci ta dalilin karanta Al'qur'ani mai girma.

Gaskiya ta bayyana: Yadda wani baturen farfesan lissafi ya musulunta bayan nazarin Al-qur'ani
Gaskiya ta bayyana: Yadda wani baturen farfesan lissafi ya musulunta bayan nazarin Al-qur'ani
Asali: Facebook

KU KARANTA: An hana wasu musulmai sallah 5 a rana a Indiya

Legit.ng Hausa cewa Mista Jeffery ya kara da cewa ya shiga musulunci ne bayan ya hadu da wani mutum mai matukar kamala a Jami'ar San Francisco mai suna Mahmoud Qandeel daga kasar Saudiyya wanda kuma abota da shakuwa suka shiga tsakanin su.

Ya cigaba da cewa abokin nasa, Mahmoud Qandeel shine ya bashi kyautar Al'qur'ani mai girma wanda yaje yayi nazari ya kuma samu amsoshin kusan dukkan tambayoyin dake gare shi game da gasgatuwar samuwar Allah mai tsarki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel