Ku cafke duk wanda ya furta kalaman batanci ko waye shi - Umurnin Buhari ga jami'an tsaro
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi abokan hamayya da su kauracewa jefa rudani a cikin jama'a ta hanyar furta kalaman batanci ko yada jita jita
- Buhari ya samu wakilcin daraktan watsa labarai na hukumar jami'o'i ta kasa, Mr. Ibrahi, Yakasai, ya ce irin ci gaba da kasar ke samu, ba za a bari kalaman batanci su tarwatsa shi ba
- A nashi bangaren, shugaban jami'ar ta Uyo, Farfesa Enefiok Essien, ya ce dalibai 4,539 ne jami'ar ta yaye, da suka hada da 631 daga PGS, sai masu digiri 3,678
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi abokan hamayya da su kauracewa jefa rudani a cikin jama'a ta hanyar furta kalaman batanci ko yada jita jita. Buhari wanda ya je jami'ar Uyo a matsayin bako na musamman, an ruwaito shi yana gargadin a bukin yaye daliban jami'ar karo na 24.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya samu wakilcin daraktan watsa labarai na hukumar jami'o'i ta kasa, Mr. Ibrahi, Yakasai, ya ce irin ci gaba da kasar ke samu, ba za a bari kalaman batanci su tarwatsa shi ba.
Ya ce, jami'o'i wasu farfajiya ce ta mutane masu zurfin tunani, wadanda ya kamata suna zama kamar wasu fitulun haska rayuwar al'umma, musamman wajen yanke hukunci, ganin cewa babban zaben 2019 na karatowa, akwai bukatar mutane su shiga taitayinsu kan furta kalaman batanci.
KARANTA WANNAN: Lafiya jari: Shin kana fama da cutar Olsa? Ka gwada sinadarin 'yayan kankana

Asali: Facebook
Ya ce gwamnatin tarayya ba zata lamunce kalaman da za su iya haddasa rikici, tsoro ko kawo sabani da gaba a tsakanin jama'a ba, kuma za ta dauki mataki akan koma waye aka samu da aikata wannan laifi.
Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin duk mai yiyuwa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'ar kasar.
Shugaban kasar ya ce: "A wannan gabar, ina so kowa ya fahimta, cewar gwamnatin tarayya ba za ta taba kyale mutanen da kalamansu ka iya hadda rikici, ko batanci da zai harzuka jama'a har hakan ya jawo tashin hankula ba, ba zamu kyale kowaye ba.
"Ya zama wajibi jami'an tsaro su gano tare da cafke duk wanda ya furta kalmar batanci, ko wanda ya haddasa sabani a tsakanin jama'a, ko ya shiga kafafen watsa labarai ya yada kalaman karya ko cin zarafi, ko haddasa zanga zanga da juyin juya hali.
"Ya zama wajibi mu ci gaba da zama tare a matsayin 'yan uwa, al'umma daya," a cewar shugaban kasar.
A nashi bangaren, shugaban jami'ar ta Uyo, Farfesa Enefiok Essien, ya ce dalibai 32 sun kammala karatunsu da matakin farko na First Class a taron yaye daliban karo na 24. Essien ya ce dalibai 4,539 ne jami'ar ta yaye, da suka hada da 631 daga PGS, sai masu digiri 3,678, da kuma 'yan kusa da digiri 230.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng