Sanata Zarewa ya tarkata a fice daga APC

Sanata Zarewa ya tarkata a fice daga APC

Tsohon sanata kuma dan takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano wanda ya nemi takarar mazabar Ko ta kudu, Sanata Isa Yahaya Zarewa a ranar Litinin, 22 ga watan Oktoba ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar mai mulki.

Da yake maga ga manema labarai a Kano kan hukuncin da ya yanke, Zarewa ya bayyana cewa ya sauya sheka ne saboda rashin adalci da aka yi wa mutane da dama a zaben fidda gwani don kawai shugabannin jam’iyyar na son daura zabin su.

Sanata Zarewa ya tarkata a fice daga APC
Sanata Zarewa ya tarkata a fice daga APC
Asali: Depositphotos

A cewarsa, mafi akasarin masu fafutuka a jam’iyyar sun yake shawarar barin jam’iyyar ne saboda rashin adalci da aka yi masu.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Sanatan APC mai ci ya fita daga jam'iyyar

Zarewa wanda ya kara da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya kara da cewa sun yanke shawarar zuwa kotu kan dalilin, amma sun kafa wani kwamiti da zai nema masu mafita.

A baya mun ji cewa aruruwan magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun fito unguwannin jihar Katsina don yin zanga-zanga kan tsarin zaben fidda gwani.

Legit.ng ta tattaro cewa magoya bayan jam’iyyar sun gudanar da zanga-zanga cikin lumana a mazabar Dustinma/Kurfi kan gudanar da zaben fidda gwani na majalisar dokokin kasar ba bisa ka’ida ba a jihar.

Da suka kai mamaya sakatariyar APC a karamar hukumar Dutsinma, masu zanga-zangan sun ce wasu dake ji da kari mulki sun yi yadda suka ga dama a zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng