Biliyoyi: Alkaluman kudin da APC ta samu daga sayar da fam din takara

Biliyoyi: Alkaluman kudin da APC ta samu daga sayar da fam din takara

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta samu zunzurutun kudi da yawansu ya kai biliyan N12.635bn daga sayar da fama-faman takara na kujeru daban-daban.

Jaridar Punch ta a bayyana cewar ta gano adadin kudin da APC ta samu din bayan tattara adadin 'yan takarar da su ka sayi fam din takara a jam'iyyar tare da hada adadin kudin da su ka biya na fam din da su ka siya.

Shugaba Buhari ne kadai ya sayi fam din takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta APC a kan farashin Naira miliyan N45m.

'Yan takarar gwamna sun sayi fam din takara a kan farashin Naira miliyan N22.5m. Bincike ya tabbatar da cewar mutane 71 ne su ka sayi fam din takarar gwamna a APC. Jam'iyyar ta samu adadin kudi biliyan N3.84bn daga sayar da fam din takarar gwamna kawai.

Biliyoyi: Alkaluman kudin da APC ta samu daga sayar da fam din takara
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, AdamsOshiomhole
Asali: Depositphotos

'Yan takarar majalisar dattijai 386 ne su ka sayi fam din takara a kan Naira miliyan N7m kowanne fam. Jam'iyyar ta samu adadin kudi biliyan N2.702bn daga sayar da fam din takarar Sanata kawai.

Akwai ragowar 'yan takara 1,587 da su ka biya Naira miliyan N3.8m domin sayen fam din takara. Adadin kudin da jam'iyyar ta samu daga wadannan 'yan takara ya kai kimanin biliyan N6.03bn.

Idan aka tattara dukkan wadannan biliyoyi sun kai biliyan N12.625.

DUBA WANNAN: Matasan arewa sun bukaci Atiku ya daina hulda da tsohon ministan PDP ko su kware masa baya

Kokarin jaridar Punch na jin ta bakin sakataren yada labaran jam'iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, bai yiwuwa ba har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewar ta kara kudin fama-faman takara ne domin samun isassun kudin da zata gudanar da zabukan cikin gida da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel