Hawa Yinusa, matar da ke jagorantar fashi da satar mutane ta shiga hannu

Hawa Yinusa, matar da ke jagorantar fashi da satar mutane ta shiga hannu

- Jami'an 'yan sanda sun cafke wata mata, Hawa Yinusa, da ke jagorantar kungiyar wasu gungun gagararrun 'yan fashi da garkuwa da mutane a hanyar Abuja-Nasarawa-Jos

- An kama Hawa, 'yar asalin jihar Nasarawa, yayin da ta je banki domin fitar da kudi daga asusun Aisha, matar da aka samu motar ta a wurinsu

- Kakakin rundunar 'yan sanda, Jimoh Moshood, ya bayyana cewar zasu gurfanar da su a gaban kotu ba tare da wani bata lokaci ba

Jami'an 'yan sanda sun cafke wata mata, Hawa Yinusa, da ke jagorantar kungiyar wasu gungun gagararrun 'yan fashi da garkuwa da mutane a hanyar Abuja-Nasarawa-Jos

An kama Hawa ne tare da wasu abokan aikinta na ta'addanci guda biyu; Nura Dahiru da Buhari's Hamisu. An kashe wani daga cikin 'yan tawagar ta bayan musayar wuta da jami'an tsaro.

Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewar sun samu manyan bindigu samfurin AK-47 guda uku, alburusai da kuma wata mota mallakar wata mata 'yar kasuwa, Aisha Haruna, da ta fada tarkonsu, duk a wurin su.

Hawa Yinusa, matar da ke jagorantar fashi da satar mutane ta shiga hannu
Hawa Yinusa da wanda aka kama su tare
Asali: Instagram

An kama Hawa, 'yar asalin jihar Nasarawa, yayin da ta je banki domin fitar da kudi daga asusun Aisha, matar da aka samu motar ta a wurinsu.

'Yan sanda sun bayyana cewar 'yan ta'addar sun kashe Aisha tare da yasar da gawar ta a wani jeji da ke kauyen Uke a jihar Nasarawa.

DUBA WANNAN: Rikicin Kaduna: Buhari ya fusata, ya sanar da matakin da zai dauka

"Hawa ta je kotu tare da yin rantsuwa cewar Aisha 'yar uwarta ce kuma an kama ta ne a lokacin da ya rage saura kiris ta fitar da miliyan N1m daga asusun marogayiya Aisha," kamar yadda Jimoh Moshood, kakakin hukumar 'yan sanda na kasa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

Moshood ya cigaba da cewa, "Hawa da ragowar yaranta sun dade su na aikata fashi da sace matafiya a kan hanyar Abuja, Nasarawa da Filato. Sun amsa cewar sun sha karbar katin cirar kudi (ATM) tare da zuwa su cire kudin da ke cikin asusun mutum kafin su sake shi. Wasu daga cikin wadanda su ka taba yiwa hakan sun gane su, kuma su ma sun amsa aikata yin hakan."

Kakakin rundunar na 'yan sanda ya bayyana cewar zasu gurfanar da su a gaban kotu ba tare da wani bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng