Tsohon CJN Idris Kutigi ya bar Duniya yana da shekaru kusan 80 da haihuwa

Tsohon CJN Idris Kutigi ya bar Duniya yana da shekaru kusan 80 da haihuwa

Dazu nan labari ya shigo mana daga Jaridar Punch ta Kasar nan cewa Tsohon Shugaban Alkalan Najeriya Idris Kutigi ya cika. Babban Alkalin ya rasu ne a wani asibiti da ke Garin Landan a Ingila bayan rashin lafiya da yayi.

Tsohon CJN Idris Kutigi ya bar Duniya yana da shekaru kusan 80 da haihuwa
Babban Alkali Idris Kutigi ya bar Duniya bayan rashin lafiya
Asali: UGC

Babban Yaron Alkalin Alkalan kasar watau Sani Kutigi shi ya tabbatarwa ‘Yan Jarida rasuwar Mahaifin na su. Idris Kutigi ya cika ne a kasar waje bayan yayi ‘yar budurwar rashin lafiya inda yayi jinya a wani babban asibiti a Kasar Birtaniyya.

An haifi Idris Kutigi ne a karshen shekarar 1939 inda ya kai kololuwar aikin sa a 2007 bayan da aka nada sa Alkalin Alkalai na Najeriya. Alkali mai shari’a Kutigi ya rike wannan mukami ne har zuwa karshen 2009 lokacin da yayi ritaya.

Kamar yadda mu ka samu labari, Mai shari’a Idris Kutigi ya rasu ya bar ‘Ya ‘ya 18 da kuma Jikoki fiye da 40. Kutigi ya rike mukamin Kwamishinan shari’a a Jihar Neja kafin a nada sa Alkalin babban Kotun Tarayya a cikin shekarar 1976.

KU KARANTA: Ya kamata Likitocin mu da ke waje su dawo Najeriya domin ayi gyara - Buhari

Babban Mai shari’ar ya soma aiki da Kotun koli ne a 1992 inda ya shafe shekaru da-dama. Daga baya kuma dai aka aika sunan babba Alkalin ya maye gurbin Salihu Alfa Belgore a matsayin Shugaban Alkalai na Najeriya gaba daya.

Yanzu haka dai Iyalin Marigayin su na shirya yadda za a dawo da gawar mamacin Najeriya domin ayi masa sallah. Sani Kutugi ne ya bayyanawa manema labarai hakan ba da jimawa ba. Asalin Kutigi 'Dan Jihar Neja da ke Arewacin Kasar.

Dazu kun ji cewa kwamitin da aka nada tayi bincike game da makaman Jami’an tsaron da su kayi dabo a kasar nan ta bayyana cewa bindigogi fiye da 50 su ka bace daga hannun ‘Yan Sandan Najeriya daga 2016 zuwa 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel