Na hannun daman Atiku ya bayar da haske a kan yankin da zasu dauko mataimaki

Na hannun daman Atiku ya bayar da haske a kan yankin da zasu dauko mataimaki

A yayin da hukumar zabe ta tsayar da gobe, Laraba, a matsayin ranar karshe ta karbar sunayen 'yan takara, zababben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai zabo abokin takararsa daga yankin kudu maso yama na 'yan kabilar Yoruba.

Wani na hannun damar Atiku da ke cikin taron da ake yi domin zaben wanda zai zama mataimaki ga dan takararsu, ya bayyana cewar duk da su na sane da cewar yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo na son kujerar, akwai dalilai 3 da ya sa tilas su mika kujerar ga yankin kudu maso maso yamma.

"Tabbas tunaninmu na zaben mataimaki a tsakanin yankin kudu maso gabas da yankin kudu maso yamma. Dole akwai abubuwan dubawa saboda kujerar mataimaki ba maganar siyasa ba ce kawai. Mu na bukatar wanda zai taka irin rawar da Osinbajo ke takawa a gwamnatin APC," kamar yadda majiyar mu ta bayyana mana.

Na hannun daman Atiku ya bayar da haske a kan yankin da zasu dauko mataimaki
Atiku
Asali: Facebook

Sannan ya kara da cewa, "mu na duba irin gudunmawar da mataimakin zai bawa takarar mu, wannan shine dalilin da yasa har yanzu bamu bayar da sanarwar abokin takarar Atiku ba, hakan ne kuma ya saka mu canja shawarar daukan mataimaki daga yankin kudu maso yamma.

"Na farko, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Jonathan a PDP, ba a dama da yankin kudu maso yamma ba. Pius Anyim; sakataren gwamnati daga yankin kudu maso gabas ya fito, Namadi Sambo; mataimakin shugaban kasa, dan arewa ne, haka shugaban majalisar dattijai, David Mark da takwaransa na majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal.

DUBA WANNAN: Buhari ya rubuta wasika zuwa ga Saraki, ya ki rattaba hannu kan wasu kudiri 15

"Bayan haka, yankin kudu maso yamma shine ke da yawan jama'a masu kada kuri'a bayan arewa, ka ga dole mu duba wannan batu saboda so mu ke mu samu kuri'u mafi rinjaye daga kowanne yanki.

"Abu na uku shine, dole mu samo wani mutum mai ilimi kuma gogagge kamar Osinbajo domin ta hakan ne kadai zamu samu kuri'u masu yawa daga jama'ar yankin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel