Siyasa mugun wasa: Murnar Sanata Shehu Sani ta koma ciki game da zaben fidda gwani

Siyasa mugun wasa: Murnar Sanata Shehu Sani ta koma ciki game da zaben fidda gwani

A ranar juma’a 5 ga watan Oktoba ne uwar jam’iyyar APC ta fitar tare da tabbatar da sahihin jerin sunayen yan takarkarun mukamin kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya da aka dade ana takaddama akan sunayen.

Legit.ng ta ruwaito an samu takaddama game da sunayen yan takarar da zasu fafata a wannan zabe na fitar da gwani a satin daya gabata, inda wata takarda mai kunshe da sunayen wasu yan takara ta bayyana dake dauke da sunan Shehu Sani, amma babu na abokin hamayyarsa, Uba Sani.

KU KARANTA:Karshen alewa kasa: Allah ya tona asirin wani tsoho dake aikata luwadi da yara

Fitiwar wannan jerin sunaye ya janyo cece kuce a tsakanin yan takarar da suke ganin ba ayi musu adalci na da magoya bayansu, wanda har ta kai ga guda daga cikin yan takarar ya shigar da kara gaban kotu.

Sai dai a wani hannun kuwa, Sanata Shehu Sani da magoya bayansa sun bayyana farin cikinsu da wannan sunaye, wanda hakan ke alanta shi kadai ne zai tsaya takarar ba tare da hammayya ba, amma kash! Murna ta koma ciki.

Murna ta koma ciki ne saboda tun bayan fitar wancan sunaye ne gwamnan jahar Kaduna, kuma wanda basa ga maciji da Sanata Shehu Sani ya shiga yin korafi, har da zuwa fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari duk dai akan wannan magana, kamar yadda Shehun da kansa ya tabbatar.

Zuwa yanzu dai a iya cewa bukatar Gwamna Nasir El-Rufai ta biya, tunda a yau ne jam’iyyar ta fitar da sabbin sunayen yan takarar, takardar da ta samu sa hannun shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshimole ta bayyana sunayen yan takarar da zasu fafata a zaben fidda gwani da za’a yi a ranar Asabar.

Yan takarar da APC ta amince dasu akwai Suleiman Abdu Kwari, Abba Armaya’u, da Aliyu M Lawal daga sanatoriya ta daya, sai Uba Sani, Shehu Sani, Shamsuddeen Shehu Giwa, Muhammad Sani Saleh da Ibrahim Giwa daga sanatoriya ta biyu sai kuma Barbanas Bantex da Zagi Caleb daga sanatoriya ta uku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel