Kabilanci: An bada karin bayanai kan kashe-kashen Jos a makon jiya zuwa yau

Kabilanci: An bada karin bayanai kan kashe-kashen Jos a makon jiya zuwa yau

- Hukumar jami'ar jihar Filato ta bayyana cewa rikicin da ake a sassan jihar yayi sanadin mutuwar dalibin ta

- Hukumar ta karyata jita jitan da ake yadawa na cewa dalibai 7 ne suka rasa rayukan su

- Amma biyu daga cikin daliban su samu raunuka, wani daya kuma ya bata

Kabilanci: An bada karin bayanai kan kashe-kashen Jos a makon jiya zuwa yau
Kabilanci: An bada karin bayanai kan kashe-kashen Jos a makon jiya zuwa yau
Asali: Depositphotos

Hukumar jami'ar jihar Filato ta bayyana cewa daya daga cikin daliban ta ya rasa ran shi a rikicin da ke faruwa a wasu sassan jihar.

Mataimakin registrar din makarantar, Abdullahi Abdullahi ya karyata jita jitan da ke yaduwa a shafukan sada zumunta na cewa dalibai 7 ne suka rasa rayukansu. Amma ya jaddada cewa an kashe dalibi daya, biyu kuma sun samu raunuka, inda daya kuma ya bace.

Hukumar makarantar ta hori dalibai da malamai dasu kiyaye, tare da bin umarnin jami'an tsaro.

Ya kara da bayanin cewa gawar dalibin na mutuware, an sallami daya daga cikin masu raunikan, dayan kuma yana karbar taimakon likitoci.

Domin girmama iyayen daliban, hukumar makarantar taki sanar da sunayen daliban da iftila'in ya fada ma wa amma Idan bukatar hakan ta taso, zata sanar.

Hukumar ta tabbatar da cewa zata hada kai da cibiyoyin tsaro tare da Gwamnatin jihar don cigaba da tsare dukiyoyi da rayukan al'ummar jami'ar.

DUBA WANNAN: Nuhu Ribadu ya dawo takarar gwamna

Majiyar mu ta sanar damu cewa an sa matakan tsaro masu karfi a jami'ar domin sojoji da jami'an yan sanda ke tsare dasu.

Gwamna Simon Bako Lalong, a ranar litinin da dare yayi taro da shuwagabannin cibiyoyin tsaron jihar domin kawo karshen rikicin dake addabar jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel