Mai rabo ka dauka: APC ta amince da takarar mutane 3 da ke burin kayar da gwamna Abubakar

Mai rabo ka dauka: APC ta amince da takarar mutane 3 da ke burin kayar da gwamna Abubakar

- An tantance masu neman takarar kujerar gwamna hudu daga jihar Bauchi

- Akwai 'yan takara uku a jihar da ke kokarin kawar da gwamna Abubakar mai ci a yanzu

- Za ayi amfani da tsarin kato bayan kato ne wajen gudanar da zaben fitar da gwanin

Jam'iyyar APC ta tantance gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar, Farfesa Mohammed Ali Pate, Captain Bala Jibrin da Dr. Ibrahim Yakubu Lame a hedkwatan jam'iyyar da ke Abuja domin fafatawa a zaben fitar da gwani da za'a gudanar a ranar Asabar.

Gwamnan Mohammed Abubakar mai ci a yanzu zai fafata da 'yan takarar guda uku domin neman samun tikitin takarar jam'iyyar.

Mai rabo ka dauka: APC ta amince da takarar mutane 3 da ke burin kayar da gwamna Abubakar
Mai rabo ka dauka: APC ta amince da takarar mutane 3 da ke burin kayar da gwamna Abubakar
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Fitar da 'yan takara: APC ta nada gwamnoni a matsayin jami'an zabe

Pate, Lame da Jibrin da magoya bayansu sun dau alwashin kayar da gwamna Abubakar a zaben fitar da gwani da za'a gudanar a jihar.

A baya, 'yan takarar uku sun bayyana cewa za su hada kai waje guda domin marawa daya daga cikinsu baya ya tunkari gwamna a zaben fitar da gwanin a lokacin da jam'iyyar ta ce za tayi amfani da deleget wajen gudanar da zaben.

Sai dai daga baya, hedkwatan jam'iyyar na kasa ta bayar da umurnin cewa wasu jihohin ciki har da Bauchi su yi amfani da tsarin kato bayan kato wajen gudanar da zaben fitar da 'yan takararsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel