Kato bayan kato: Ana gudanar da zaben tsayar da dan takarar shugaban kasa na APC (Hoto)

Kato bayan kato: Ana gudanar da zaben tsayar da dan takarar shugaban kasa na APC (Hoto)

A yau ne ake gudanar da zaben cikin gida na tsayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, zaben da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kadai dan takarar daya tsaya don zarcewa akan kujerar daya shafe sama da shekaru uku yana kai.

Legit.ng ta ruwaito an samu yayan jam’iyyar APC da dama da suka fita don kada kuri’unsu a wannan zabe, zaben da ake shiryashi akan tsarin kato bayan kato don baiwa yayan jam’iyyar damar zaban yan takarkarunsu da kansu.

KU KARANTA: Buhari ya tattauna da yan Najeriya mazauna kasashen waje bayan sun karrama shi

A mahaifar Buhari dake garin Daura ma jama’a maza da mata sun yi dafifi a akwatin da shugaban kasa Buhari ka kada kuri’arsa dake mazabar Sarkin Yara, don mara ma dansu baya ya cigaba da mulkin Najeriya har zuwa shekarar 2023.

Idan za’a tuna jam’iyyar APC ta sanar da yin amfani da tsarin kato bayan kato wajen fitar da yan takarar shugaban kasarta, sa’nnan ta umarci rassanta na jahohi dasu yi amfani da duk tsarin da yafi musu, walau na kato bayan kato hajiya bayan hajiya ko kuma na wakilai watu daliget.

A yayin da ake gudanar da zaben shugaban kasa, ana sa ran jam’iyyar zata gudanar da zaben fitar da gwani na yan takarkarun gwamnoni zuwa ranar Asabar 29 ga watan Satumba.

A wani labarin kuma shugaban kasa Buhari ya shaida ma yan Najeriya mazauna kasar waje cewa shi kadai ne dan takarar shugaban kasa, inda yace sauran abokan takararsa sun tsere daga jam’iyyar, amma yace zai bisu har inda duka koma ya kadasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel