Dakarun Soji sun dakile wata hari da Boko Haram suka kai a Garshigar

Dakarun Soji sun dakile wata hari da Boko Haram suka kai a Garshigar

- 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sunyi yunkurin kai hari a garin Garshigar da ke jihar Borno

- 'Yan ta'addan sun nufo garin na Garshigar ne cikin motocci masu dauke da manyan bindigu guda tara

- Sai dai Dakarun Sojojin Najeria na Operation Lafiya Dole sun fatattake su tare da halaka wasu cikinsu

Dakarun Sojin Najeriya sun yiwa mayakan Boko Haram babbar illa yayin da suka ka yi kokarin kai hari a Garshigar da ke karamar hukumar Mobar da ke jihar Borno a jiya Laraba kamar yadda majiyar sojin ta sanar.

Direktan yada labarai na Hukumar Sojin, Texas Chukwu ne ya bayar da sanarwan a ranar Alhamis a birnin Maiduguri.

Dakurun Soji sun fatattaki 'yan Boko Haram a yayin da suka kai hari a wani gari
Dakurun Soji sun fatattaki 'yan Boko Haram a yayin da suka kai hari a wani gari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwartanci: An ajiye ma'aikacin gwamnatin jihar Katsina a gidan kaso

Mr Chukwu ya ce 'yan ta'addan sun nufi garin cikin motoccin su masu dauke da bindiga guda tara amma Dakarun Bataliya ta 145 na Operation Lafiya Dole suka fatatake bayan sunyi musayar wuta kuma sojin sunyi galaba.

Ya kara da cewa nazarin da aka yi ya nuna cewa Sojin sun yiwa 'yan ta'addan lahani sosai tare da lalata motoccin su da wasu kayan yaki wanda hakan ne ya tilastawa 'yan ta'addan juyawa ba tare da shirri ba.

Direktan ya ce sojojin sun cigaba da yin sintiri a garin Garshigar da kewaye domin tabattar da cewa 'yan ta'addan ba su sake yunkurin kai harin ba.

Daga karshe ya yi kira da al'ummar karamar hukumar Mobar su kwantar da hankullansu domin dakarun sojin za su cigaba da tabbatar da cewa akwai ingantaccen tsaro a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel