Coronavirus: Kasar Saudiyya za ta maida wa masu zuwa Umra kudadensu

Coronavirus: Kasar Saudiyya za ta maida wa masu zuwa Umra kudadensu

Ma’aikatar da ke kula da aikin Hajji da Umrah a kasar Saudiyya ta sanar da cewar za ta maida wa wadanda suka yi niyar zuwa yin Umra kudadensu.

Hakan ya biyo bayan dakatar da aikin ibada da mahukuntan kasar suka yi na dan wani lokaci.

Kasar ta dauki wannan mataki ne sakamakon bullowar annobar cutar Coronavirus da ke ci gaba da bazuwa a kasashen duniya.

Coronavirus: Kasar Saudiyya za ta maida wa masu zuwa Umra kudadensu

Coronavirus: Kasar Saudiyya za ta maida wa masu zuwa Umra kudadensu
Source: Twitter

A kwanan nan ne Saudiyya ta dauki matakin dakatar da kasashen waje shiga cikinta domin gudanar da ibadah a Makkah da Madina.

Tuni dai wadanda suka biya kudin zuwa aikin Umrah suka nuna rashin jin dadinsu kan wannan yunkuri. Sai dai sun ce sun rungumi kaddara duba ga cewar lalura ce ta sanya kasar mai tsarki daukar wannan mataki.

A baya dai mun ji cewa Hukumar jin dadin alhazai NAHCON ta yi kira ga maniyyatan Hajjin bana da Umrah sun dakatad da duk wani shirye-shiryen ziyartar Makkah ko Madina har ila ma shaa’ llahu.

Kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda, ta sanar da cewa an dakatad da shirye-shiryen Umrah zuwa kasar Saudiyya ne saboda matakin da kasa mai tsarkin ta dauka wajen kare kanta daga cutar Coronavirus.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Wani farfesa dan Najeriya mai suna Farfesa Maduike Ezeibe ya sanar da cewa ya samo maganin cutar Coronavirus da zazzabin Lassa, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Farfesan a fannin 'Virology' a jami'ar Michael Okpara ta aikin noma da ke Umudike, ya taba ikirarin samo maganin cuta mai karya garkuwar jiki. Ya tabbatar da cewa tunda ya samar da maganin cuta mai karya gakuwar jikj, cutar Coronavirus za ta zama tarihi.

Azeibe ya yi kira ga kasashen duniya da muguwar cutar ta addaba a kan su gwada maganin shi a kan marasa lafiyan.

Idan za mu tuna, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta bada kudi tsaba har naira miliyan 36 ga duk dan Najeriyan da ya samo maganin cutar Coronavirus da zazzabin Lassa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel