Motar daukan yashi ta tattake wata Mata mai dauke da juna biyu a garin Jos

Motar daukan yashi ta tattake wata Mata mai dauke da juna biyu a garin Jos

Wata mata mai dauke da juna biyu ta gamu da ajalinta a daidai lokacin da wani direban bankaura yayi ciki da ita da motarsa ta daukan yashi, sa’annan ya raunata mutane hudu a garin Jos, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar a Laraba 19 ga watan Satumba da misalin karfe shida na yamma a karamar hukumar Jos ta Arewa, inda motar tayi kan mutane sakamakon lalacewar birkin motar, kamar yadda direban motar ya bayyana.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya baiwa iyalan wani Ministansa daya rasu kyautar katafaren gida

Wani shaidan gani da ido mai tuka Keke Napep, Ibrahim Ahmad ya tabbatar da cewa a gabansa motar ta take Matar; “A lokacin da direban ke kokarin rike motar, akwai wata mata mai ciki dake dauke da karamin yaro a hannunta.

“Alokacin data ga motar ta nufota, sia ta jefar da yaron a kokarinta na tserewa, amma kafin ta ankara motar ta yi ciki da ita, ta tattaketa, amma mun yi kokarin garzayawa da ita zuwa Asibitin Sunnah dake garin Jos.” Inji shi.

Sai dai likitan asibitin Sunnah, Dakta Alabi T.A ya tabbatar da cewa Matar ta riga ta mutu koda aka kaita asibitinnasu; “Tuni iyalan matar suka dauki gawarta don yi ma jana’iza, amma sauran mutane hudu da suka jikkata suna samun kulawa a asibtinmu.”

A wani labarin kuma wani mummunan hadari a cikin garin Gombe yayi sanadiyyar mutuwar mutum guda daya tare da jikkata mutane takwas, a lokacin da wata babbar mota ta yi taho mu gama da motoci da babura.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng