An caka masa: Tsohon dan majalisa ya maka Amaryarsa tare da ‘Mai dalilin aure’ gaban Kotu
Wani tsohon dan majalisa a jihar Jigawa, Alhaji Hussaini Namadi Auyo ya shigar da amaryarsa da suka kwashe sati uku kacal suna tare gaban Kotu, biyo bayan tserewa da ta yi zuwa kasar Nijar.
Namadi wanda shi ne tsohon wakilin Hadejia/Auyo/Kafin Hausa a majalisar wakilan Najeriya a inuwa jam’iyyar PDP ya shigar da kara ne ta hannun lauyansa, Barista Ukashatu Adamu, inda ya bukaci ko dai Kotu ta tilasta ma Amaryarsa Jamila komawa gidansa ko kuma ta biya naira miliyan 30 da ya kashe a aurenta.
KU KARANTA: Wasikar Obasanjo: Talakawa ne zasu zabe mu ba attajirai ba – Inji Gwamnan jihar Kaduna
Haka zalika Namadi ya kara har da matar da ta nemo masa Amarya, wato mai dalilin aure, wanda ita ma yace da hadin bakinta amaryarsa Jamila ta tsere. Barista Ukashatu yace Namadi ya bada kwangilar a samo masa budurwa fara, mai gashi, mai diri, doguwa, mai idanu dara dara, da kuma wushirya daga kasar Nijar.
Sai dai bayan an samo irin wannan mace ne, sai Namadi ya shiruya kayataccen biki, inda yayi jigilar Jamilah da yan uwanta tun daga Nijar har Najeriya don halartar bikin, amma sati uku da tarewa ta nemi izinin zuwa ganin gida, shi ne fa har yanzu ta ki dawowa.
Legit.ng ta ruwaito a duk lokacin da Namadi ya bukaci ta dawo gidansa, sai ta bukaci ya bata takardar saki, wai ba ta yi, haka ne ya sanya Namadi bukatar Kotun shari’an Musulunci dake Shahuci ta bi masa hakkinsa.
Shi kuwa lauyan Mai dalilin aure, Barista Sa’idu Tudun Wada ya bukaci kotu ta cire wacce yake wakilta daga karar, saboda a cewarsa ta riga ta gama aikinta na nema masa matar aure wanda ta cika dukkanin sharuddan da yake bukata.
Amma ganin alkalin Kotun, Garba Ahmed yayi watsi da bukatarsa, sai lauyan ya nemi a yi sulhu a wajen Kotu, inda yace zasu ya nema ma Hussaini Namadi kanwar amaryarsa, wanda ta ma ta cika dukkanin sharuddan da yake nema a jikin mace. Daga nan sai Alkali y adage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Maris.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng