Kokarin ka na farantawa musulmi da arewa rai na nuna kokarinka na musuluntar da Najeriya - CAN ga shugaban Najeriya

Kokarin ka na farantawa musulmi da arewa rai na nuna kokarinka na musuluntar da Najeriya - CAN ga shugaban Najeriya

- CAN ta zargi shugaban Buhari da nuna bambancin addini

- 'Duk mukaman da ya bada kwanan nan babu Kirista'

- 'Hakan yayi ne domin cimma wata manufa'

Kokarin ka na farantawa musulmi da arewa rai na nuna kokarinka na musuluntar da Najeriya - CAN ga shugaban Najeriya
Kokarin ka na farantawa musulmi da arewa rai na nuna kokarinka na musuluntar da Najeriya - CAN ga shugaban Najeriya
Asali: Depositphotos

Kungiyar kiristoci ta kasa ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da nuna bambancin addini. Kungiyar tace jiga jigan mukamai da ya bada kwanan nan babu Kirista ko Dan kudu mutum daya.

Kwanan nan Buhari ya zabi Yusuf Magaji Bichi, musulmi da jihar kano domin maye gurbin Matthew Seiyifa, Dan jihar Bayelsa, shugaban hukumar DSS.

Mista Umar Masanawa kuma manaja Daraktan tsaro da buga kudi na najeriya, tare da Hajiya Zainab Ahmed Waziri da ta maye gurbin Kemi Adeosun da ta ajiye aiki a satin da ya gabata.

Mai magana da yawun kungiyar kiristoci ta kasa, Bayo Oladeji, ya zargi hakan da raba kan yan kasa da ganganci.

DUBA WANNAN: Ka zarce kawai, Neja Delta ga Buhari

Yace "CAN ta fuskanci abin mamaki don shugaban na niyyar raba kan kasa daya mai addinai da yarika daban daban. Kungiyar takara nuna damuwar ta akan yanda shugaban yasa musulmai suka fi yawa a tafiyar shi da aiyuka a Gwamnatin shi."

Fadin cewa a dena korafi akan yanda ya cika Gwamnatin shi da musulmi rashin hankali ne da rashin son zaman lafiya a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel