Sheikh Nakaka ya zama sabon shugaban majalisar Malamai da Limamai ta Kaduna

Sheikh Nakaka ya zama sabon shugaban majalisar Malamai da Limamai ta Kaduna

Al Sheikh Malam Ibrahim Nakaka ya zamo sabon shugaban majalisar Malamai da Limamai na jahar Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta samu rahoto daga jahar Kaduna.

Nakaka ya dare wannan kujerar ne bayan mutuwar shugaban majalisar, Sheikh Usman Abubakar Babantune wanda ya rasu a ranar 10 ga watan Satumbar 2018 a babban asibitin koyawar na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika.

KU KARANTA: Ta fasu: an bayyana makudan biliyoyin da wani Gwamna ya kashe wajen yawo a jirgi

Sheikh Nakaka ya zama sabon shugaban majalisar Malamai da Limamai ta Kaduna
Sheikh Nakaka a tsakiya
Asali: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cikin wata sanarwa da sakataren majalisar, Malam Yakubu Yusuf Arrigasiyyu ya fitar a ranar Alhamis din makon data gabata yana cewa an zabi Nakaka ne bayan tattaunawa da yayan majalisar.

Malam Arrigasiyyu ya bayyana cewa majalisar ta zabi Dakta Muhammad Aliyu Limamin masallacin Juma’a na Zaria Lowcost a matsayin mataimakin shugaba na farko.

Hakazalika sanarwar ta kara da bayyana sunayen Limaman Masallatan Juma’a na Yahaya road Muhammad Hassan da na babban masallacin Juma’a na garin Kafanchan Muhammad Kabir Qasim a matsayin mataimakan shuwagabanni na biyu da na uku.

Daga karshen sanarwar, Arrigasiyyu yayi kira ga yayan majalisar dasu jajirce tare da hada hannu wajen gudanar da aiki tukuru wajen ciyar da addinin Musulunci gaba a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng