Buhari, Tinubu da shugabanin APC na kudu maso yamma sun saka labule a fadar Aso Villa

Buhari, Tinubu da shugabanin APC na kudu maso yamma sun saka labule a fadar Aso Villa

Shugaban jam'iyya na jam'iyyar PDP, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya jagorancin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC wajen wata ganawa tare da shugaba Muhammadu Buhari a yammacin yau Alhamis, 30 ga watan Augusta.

Punch ta ruwaito cewa anyi taron ne a dakin taro na uwar gidan shugaban kasa da ke fadar Aso Villa. An fara taron ne misalin karfe 8.30 na yamma inda aka fara da tattauna batutuwan da suka shafi zaben Osun gwamna na jihar Osun da za'a gudanar a ranar 22 ga watan Satumban wannan shekarar.

Bayan gama taron 'kusoshin APC', Tinubu da shugabanin kudu maso yamma sun kebe da Buhari
Bayan gama taron 'kusoshin APC', Tinubu da shugabanin kudu maso yamma sun kebe da Buhari
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa

Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Ciyaman din jam'iyyar APC na kasa, Adams Osiomhole suma sun hallarci taron.

Sauran wadanda suka sami hallaratan taron sun hada da gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo da takwaransu na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Ciyaman din kwamitin yakin neman zabe na takarar gwamnan jihar Osun na wannan shekarar, gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano shima ya hallarci taron.

Ana cigaba da gudanar da taron a lokacin da aka rubuta wannan rahoton.

Ku biyo mu domin karin bayani...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel