Rabonsu ya rantse: Gwamnatin jahar Kaduna na neman teloli don ta basu kwangila

Rabonsu ya rantse: Gwamnatin jahar Kaduna na neman teloli don ta basu kwangila

A cigaba da kokarinta na yin garambawul a fannin ilimi, gwamnatin jahar Kaduna a karkashin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sanar da neman telolin da zata basu kwangilar dinkin kayan yan makarantun sakandari a jahar.

Legit.ng ta ruwaito gwamnatin ta sanar da haka ne cikin wata sanarwar data fitar a jaridu, inda ta bukaci dukkanin telolin dake da sha’awar samun wannan kwangila dasu aika takardun nuna bukatarsu ga ma’aikatan ilimi ta jahar

KU KARANTA: Bafarawa ya yi watsi da duk wani tayin sulhu da sauran yan takarar shugaban kasa

Idan za’a tuna a baya kusan shekaru biyu da suka shude gwamnatin jahar ta bada kwatankwacin wannan kwangilar, kuma teloli da dama sun amfana, amma fa aikin yazo da matsaloli da kalubale daban daban.

Telolin da suka yi wannan aiki a wancan lokaci sun koka kwarai da gaske kan yadda ba’a basu kwangilar kai tsaye, sai dai subi ta hannnun yan siyasa da suka yi kane kane, wanda ya janyo daukan tsawon lokaci kafin tela ya samu kudinsa.

Sai dai a wannan karon, gwamnatin jahar ta bayyana cewa ta samar da tsare tsare da zasu samar da ingantaccen yanayi don kauce ma matsalolin da aka samu a baya inji mai magana da yawun gwamnatin, Samuel Aruwan.

Rediyon bbc hausa ta ruwaito Aruwan yana cewa a yanzu an nemi kowanne tela ya mika lambar asususn bankinsa da na BVN, hakan na daga cikin sharadin samun aikin, sa’annan yace aikin zai fi karkata ga matasa ne don kara musu kwarin gwiwa akan sana’arsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel