Gargadi: Jihohin Najeriya 7 zasu fuskanci ambaliyar ruwa - NIHSA

Gargadi: Jihohin Najeriya 7 zasu fuskanci ambaliyar ruwa - NIHSA

Hukumar nazarin yanayin ruwa na Najeriya (NIHSA) ta ce akwai yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa daga rafin Neja wanda zai shafi jihohin da ke makwabtaka da rafin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Direktan injiniyoyi na NIHSA, Clement Eze ya ce a halin yanzu matatarar ruwa ta Kainji da Jebba sun cika sun batsu har sun fara ambaliya sannan adadin ruwa a rafin Lokoja da ke jihar Kogi ya dara adadin ruwa a shekarar 2012.

Gargadi: Jihohi 7 da ambaliyar ruwa zai shafa a Najeriya - NIHSA
Gargadi: Jihohi 7 da ambaliyar ruwa zai shafa a Najeriya - NIHSA
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ana zargin Tambuwal da yiwa Wamakko bita da kulli

Kamar yadda sanarwan ta ce, akwai yiwuwar ambaliyar ruwan za ta shafi jihohin da ke kewaye da rafin Neja a yankin Arewa ta tsakiya, Kudu maso Kudu da wasu sassan Kudu maso gabashin kasar.

Jihohin da ake kyautata zaton ambaliyar zai shafa sune:

1. Jihar Kebbi

2. Jihar Neja

3. Jihar Kwara

4. Jihar Kogi

5. Jihar Anambra

6. Jihar Delta

7. Jihar Bayelsa.

Kazalika, sanarwan ta kuma ce ambaliyar da ta afku a jihar Kaduna a ranakun 23 da 24 na watan Augustan 2018 ya fara bulla matatarar ruwa ta Shiroro wanda itama ta fara ambaliya wanda hakan na barazana da garuruwan da ke kusa ta tafkin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel