Kingiyar kabilar Igbo (Ohanaeze) tayi kakkausan gargadi ga gwamnatin Buhari

Kingiyar kabilar Igbo (Ohanaeze) tayi kakkausan gargadi ga gwamnatin Buhari

A jiya, Asabar, ne kungiyar 'yan kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, tayi kausasan kalamai tare da yin gargadi ga gwamnatin tarayya a kan wasu mata 112 'yan kabilar Igbo yayin da suke gudanar da wata zanga-zanga tsirara ta neman a fito da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, da har yanzu ba a san inda yake ba.

Gwamnatin tarayya ce ta kama matan tare da gurfanar da su bisa tuhumar su da yin taro da ya saba da doka da kuma cin amanar kasa.

Kungiyar ta Ohanaeze ta bayyana cewar kama matan da gwamnati tayi ya nuna cewar gwamnatin tarayya tay baki biyu.

An kama matan 112 ne yayin da suke gudanar da wata zanga-zanga, rabinsu tsirara, a garin Owerri na jihar Imo, domin neman gwamnati ta gudanar da kuri'ar raba gardama da zata bawa 'yan kabilar Igbo damar zabin son su cigaba da zama a Najeriya ko sabanin haka tare da bukatar gwamnati ta sanar da su inda shugaban kungiyar masu fafutikar 'yan aware ta biyafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ke.

Kingiyar kabilar Igbo (Ohanaeze) tayi kakkausan gargadi ga gwamnatin Buhari
Shugabannin ungiyar kabilar Igbo (Ohanaeze)

Kungiyar Ohanaeze ta kafe kan cewar kama matan tamkar cin mutunci da take hakkinsu na 'yan kasa, suna masu kafa hujja da cewar gwamnatin tarayya ta zabi sasantawa da 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram amma ta gaza yin haka ga 'yan kabilar Igbo dake gudanar da zanga-zangar lumana, kamar yadda shugaban kungiyar, Cif John Nnia Nwodo, ya fada.

DUBA WANNAN: Labari mai dadi: Wani babban abun alheri ya samu 'yan gudun hijira a Zamfara

Nwodo ya kara da cewar, "da gan-gan gwamnatin tarayya ta ki bawa wani dan kabilar Igbo babban mukami a harkar tsaron Najeriya saboda su ci mutuncinmu yadda suke so. Muna son sanar da gwamnati cewar tura fa ta fara kaiwa bango, lokaci ya yi da gwamnati ya kamata ta fara mutunta 'yan kabilar Igbo."

Kazalika ya yi kira ga shugabanni 'yan kabilar Igbo da su manta da son mulki domin saka bukatar cigaba da neman 'yancin kabilar Igbo a gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel