Zaben maye gurbi a jihar arewa: PDP ta kayar da APC

Zaben maye gurbi a jihar arewa: PDP ta kayar da APC

Dan takarar jam’iyyar PDP, Mista Garba Ajiya, ya lashe zaben maye gurbi na dab majalisa mai wakiltar karamar hukumat Takum a majalisar dokokin jihar Taraba da aka yi jiya, Asabar, 18 ga Agusta, 2018.

Kamfanin dillancin Labarai na kasa (NAN) ta bayyana cewar an gudanar da zaben na jiya ne domin maye gurbin tsohon dan majalisa Hosea Ibi da masu garkuwa suka sace ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2017 kuma suka kasha shi a watan janairu na shekarar 2018.

Baturen zaben hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Dakta Ayuba Kwada, ne ya sanar da sakamakon a daren jiya a karamar hukumar Takum.

Zaben maye gurbi a jihar arewa: PDP ta kayar da APC
Zaben maye gurbi a jihar arewa: PDP ta kayar da APC

Dakta Kwada ya bayyana cewar dan takarar PDP, Ajiya, ya samu nasara a mazabu 5 daga cikin 6 da karamar hukumar ta Takum ke da su da adadin kuri’u 10,725, yayin da abokin takararsa na jam’iyyar APC, Mista Atem Ansho ya samu kuri’u 3,268 da samun nasara a mazaba daya kacal.

Kazalika ya bayyana cewar an kada jimilllar kuri’u 14,717 a zaben amma 380 sun lalace tare da kin karbar sakamakon zabe daga mazabar Chanchanji saboda rashin biyayya ga dokokin zabe.

DUBA WANNAN: Tsoron tsige: Dogara da saraki zasu gudanar da zaman majalisa na hadin gwuiwa

Baturen zaben ya kara da cewar jam’iyyu 9 ne suka shiga zaben kuma an samu yawan jama’a a wurin zaben tare da nuna takaicinsa da yawan wadanda suka cika wurin zaben basu da katin zabe.

Dakta Kwada ya bukaci jama’a su yi amfani da dammar karin wa’adin bayar da katin zabe da hukumar INEC tayi domin mallakar nasu katin zaben kafin a rufe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel