Kujerar Shugaban 'Kasa: Dankwambo na neman goyon bayan wakilan PDP a Arewa maso Yammacin Najeriya

Kujerar Shugaban 'Kasa: Dankwambo na neman goyon bayan wakilan PDP a Arewa maso Yammacin Najeriya

A yayin da guguwar siyasa ke ci gaba da kadawa musamman karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, inda 'yan siyasa da dama ke hanƙoron tikitin takara na kujerar shugaban kasa, gwamnan jihar Gombe shi ma ba a bar shi a baya.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Gwamnan Alhaji Ibrahim Dankwambo, ya ziyarci jihar Kaduna domin neman goyon baya da roko sahalewar wakilan jam'iyyar ta PDP dake yankin Arewa maso Yammacin Kasar nan.

Dankwambo wanda ya bayyana sha'awar sa ƙarara a karshen makon da ya gabata, ya gana da wakilan jam'iyyar na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya domin neman amincewar su tare da goyon bayan akidar sa ta samun tikitin takarar jam'iyyar.

A yayin da yake bayyana kansa a matsayin dan takara na gasken-gaske, Dankwambo ya ce ya yi wannan kira ne sakamakon muhimmancin yankin Arewa maso Yamma wajen samun nasarar zaben shugaban kasa.

Kujerar Shugaban 'Kasa: Dankwambo na neman goyon bayan wakilan PDP a Arewa maso Yammacin Najeriya
Kujerar Shugaban 'Kasa: Dankwambo na neman goyon bayan wakilan PDP a Arewa maso Yammacin Najeriya
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya nemi wakilan jam'iyyar akan kada masa kuri'un su yayin zaben fitar da dan takara, inda ya ce ya ta tabbacin mashahurancin sa wajen samun nasara a babban zabe.

Ya kuma nemi wakilan jam'iyyar akan su tashi tsaye wajen tabbatar da al'ummar kasar nan sun mallaki katin zaben domin shine makamin su wajen fafata yakin zabe a shekarar 2019.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, shugabannnin jam'iyyar da sakatarorin su na reshen jihohin Kaduna, Kaduna, Jigawa, Kebbi, Sokoto da kuma Katsina sun halarci wannan taro.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta salwantar da $1m wajen yaso 'Yan Najeriya daga 'Kasar Rasha

Legit.ng ta fahimci cewa, Dankwambo na adawa ta hankoron tikitin jam'iyyar tare da tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal.

Sauran manema tikitin jam'iyyar sun hadar da da tsaffin gwamnonin jihar Kano biyu, Sanata Rabi'u Kwankwaso da Mallam Ibrahim Shekarau da kuma tsaohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng