Hukumar Sojin Najeriya ta shawarci Shekau ya mika wuya

Hukumar Sojin Najeriya ta shawarci Shekau ya mika wuya

- Ta ce babu wani wurin da ya rage ma sa ya buya, mika wuya ita ce kawai mafita gare shi

- Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas Rogers, shi ne ya bayyana hakan

- Ya ce rundunar ta yi kane-kane a dajin Sambisa don tabbatar da ta fatattaki sauran 'yan Boko Haram da su ka rage

Kwamandan Rundunar Soji na Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas Rogers, ya shawarci Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram, da ya mika wuya ga Rundunar Sojin. Don kuwa ya ce babu wata mafita gareshi face mika wuyar.

Hukumar Sojin Najeriya ta shawarci Shekau ya mika wuya
Hukumar Sojin Najeriya ta shawarci Shekau ya mika wuya

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba yayin zantawa ga manema labarai na kowace wata. Kwamandan ya ce Rundunar ta samu gagarumin nasara kan Boko Haram don kuwa ta kashe fiye da 186 daga cikin wadanda su ka yi saura, fiye da 1000 kuma sun mika wuya.

KU KARANTA: NAFDAC ta garkame gidajen gasa mummuki guda 24 a Borno

Ya kuma ce Rundunar ta murkushe cibiyar sansanin kungiyar a Sambisa watau ''Camp Zairo''. Ya ce a wannan karon, rundunar za ta kasance da zama a dajin har sai babu wani wurin buya ga 'yan kungiyar. Ya kuma tabbatar da cewar rundunar ta yi kane-kane a dajin, ta kuma jajirce kan kawo karshen 'yan ta'addan.

Nicholas ya kuma ce za a fitar da tituna daga Sambisa wadanda za su hadu da al'ummomi don mayar da dajin cikakken wurin zama. Sai dai kuma a halin yanzun an tsakaita tafiye tafiye a wasu manyan tituna saboda irin aiki na fatattakan 'yan ta'addan da rundunar ke yi.

A cewar sa, a shirye su ke don tabbatar da hanyoyin sun samu cikakken tsaro ta yadda mutane za su rinka tafiye-tafiyen su kan hanyoyin ba tare da wata rakiya daga soji ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164