Mu zamu kafa gwamnati a badi - Sule Lamido
- Sule Lamido na ziyarar siyasa a jihar Ogun
- Yana ganin sun kusa dawowa mulki
- Ana zarginsa da almundahana da wawurar kudin jama'a
Tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido, jagoran siyasar PDP a arewa, kuma tsohon dan siyasar a tsofin jam'iyyu da jamhuriyyoyi tun su Nehu, yace sun kusa dawowa mulki a PDP duk da a yanzu ana zargin jam'iyyarsu da wawura da sata.
A cewarsa, su zasu kafa mulki a Abuja da sauran jihohi a badi.
Saura wata 10 a dauki sabon mulki na 2019-2023 a kasar nan a siyasance.
Yana ziyarar aiki ne da tarukan jam'iyyar PDP a jihar Ogun ta Obasanjo.
DUBA WANNAN: Ba kudin da muka bayar don tsige Saraki
Ana zargin Alh. Sule da yaransa maza da satar kudaden kauyawan jiharsa ta Jigawa a lokacin yana mulki daga 2007 zuwa 2015.
Yanzu yana neman kujerar shugaban kasa a 2019 a PDP.
Shekarunsa akalla 72 shima kamar su Atiku da Buhari.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng