Kudirin masu sauya sheka shine son dakatar da tazarcen Buhari – Ndume

Kudirin masu sauya sheka shine son dakatar da tazarcen Buhari – Ndume

Sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Nduyme, ya caccakiwasu abokan aikinsa da suka sauya sheka daga jamiyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Da yake Magana da manema labarai a Maiduguri a ranar Asabar, Ndume yayi bayain cewa mai akasarinsu na da tuhuma da ake yi masu akan rashawa don haka suke yin duk yadda za su yi don ganin shugaban kasar bai zarce ba a 2019.

A cewar Ndume suna kokarin ganinBuhari bai kai labara ba domin kada aga gundun kashin da suke makale da shi.

Kudirin masu sauya sheka shine son dakatar da tazarcen Buhari – Ndume

Kudirin masu sauya sheka shine son dakatar da tazarcen Buhari – Ndume

Ndume ya kuma ba’a ga jam’iyyar PDP inda ya kira tad a matacciyar jam’iyya tar da mutane 12 dake neman tikitin takarar shugabancin kasa duk a yunkurinsu na son tsige Buhari.

KU KARANTA KUMA: Kwamishina da wasu mutane 4 na hararar kujerar mataimakin gwamnan Kano

Ya kuma jadadda cewa duk da tarin sauya shekar masu fada aji kamar su shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki suka yin a barin APC, ba zai taba shafar takarar Buhari ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel