Yadda Sanatocin APC ke yunkurin tsige Saraki – R-APC
Kungiyar sabuwar APC ta yi zargin cewa fadar shugaban kasa ta kammala shirye-shirye don sa wasu santoci tsige shugaban majalisar datawa, Dr. Bukola Saraki.
A wata sanarwa da gamayyar kungiyar dauke da sa hannun kakakinta na kasa, Prince Kassim Afegbua, ta yi zargi cewa daga cikin makarkashiyae da aka shirya shine zuwa ga wasu sanatocin PDP, musamman wadanda keda zargin rashawa aansu domin su wanke su da zaran sun sauya sheka zuwa APC.
APC ta karyata zagin a matsayin ihun mutumin dake nitsewa a koi. Tayi iirarin cewa hakan ba komai bane face bakin fenti don bata sanan jam’iyya mai mulki.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar All Progressives Congress APC ta jaddada kudirinta na son tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki daga kan kujerarsa, amma tace maimakon kashe miliyoyin naira na jama’a akan lamarin, zata yi amfani da karfinta na masu rinjaye wajen tsige Saraki daga gabanta.
KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Osinbajo da Oshiomhole na shirin hargits majalisar dokoki – Majalisar wakilai
Jam’iyyar na maida martani ga tuntubar da kafofin watsa labarai sukayi game da zargin da gamayyar kungiyar, wato sabuwar APC tayi na cewa jam’iyyar na amfani da kudin jama’a waje akai.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng