Yanzu-Yanzu: Sabon rikici ya barke a jihar Filato har an kashe mutum 3
Labarin da muke samu da dumi-dumin sa yanzu na nuni ne da cewa sabon rikici ya sake barkewa a unguwar Zanwra ta karamar hukumar Bassa dake a jihar Filato a tsakanin wasu da ake zargin makiyaya ne da kuma al'ummar garin a daren Juma'ar da ta gabata.
Sakamakon rikicin ne kuma kamar yadda muka samu har ma an samu rasa rayukan mutane akalla 3 yayin da wasu da yawa suka jikkata ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
KU KARANTA: Kashe-kashen da akeyi na matukar damu na - Buhari
Legit.ng ta samu cewa wannan rikicin dai yazo ne yan kwanaki kadan bayan wani taron zaman lalubo hanyoyin zaman lafiya a jihar da aka gudanar a tsakanin shugabannin addinai da kuma gargajiya a jihar.
A wani labarin kuma, Karuwai a Najeriya daga jihar Anambra sun yi barazanar shiga yajin aikin da zai haramtawa dukkan abokan sana'ar su kwanciya da 'yan sandan Najeriya bisa zargin muzguna masu da suke yi a wuraren sana'ar su.
Kamar yadda muka samu, daya daga cikin karuwan da ta tattauna da wakilin majiyar mu ta bayyana cewa hakika yanzu tura ce ta kai su bango don kuwa sun gaji da irin cin kashin 'yan sandan kasar ke yi masu musamman ma a garuruwan Umunze da Orumba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng