Komai nisan jifa: Makasan Farfesa Halima sun shiga hannun 'yan sanda
- Cikin ikon Allah 'yan sanda sun cafke 'yan fashin da suka kashe tsohuwar kwamishiniyar ilimi ta Katsina
- A makon da yagabata ne dai yan fashin suka harbe Farfesar a hanyar Kaduna
Tuni 'yan sanda sun fara bincike don tattara bayanai kafin kai su kotu
Hedikwatar hukumar yan sanda ta Abuja, ta bayyana cafke mutane takwas da ake zargin suna da hannu a kashe tsohuwar kwamishinan ilimi ta jihar Katsina Farfesa Halimatu idris akan hanyarta daga Kaduna zuwa Abuja.
Kakakim hukumar ‘yan sandar na kasa Jimoh Moshood ya bayyana sunayen masu laifin kamar haka; Lawal Tukur mai shekaru 40, Sulaiman Sani mai shekaru 27, Abubakar Ahmad mai shekaru 30, Abubakar Adamu mai shekaru 33, Yahaya Musa mai shekaru 33, Kabiru Bala mai shekaru 23, Rufai Tukur mai shekaru 26, sai Shehu Audi mai shekaru 32.
Jim kadan bayan shigar su hannu Moshood ya bayyana cewa wasu daga cikin masu laifinTukur da Sani sun amsa cewa sun kashe mutane hudu yayin fashin daga ciki har da tsohuwar kwamishinan ilimin.
KU KARANTA: Abin tausayi: Barayi sun harbe wani dan canji, sun yi awon gaba da kusan miliyan 30
Ya kara da cewa masu laifin sun yi garkuwa da mata guda biyu; Rahinatu Shehu mai shekaru 51, sai kuma Aisha Sani ‘yar shekara 23 wanda duk suke zaune a garin Maraba-Guga dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
An kama masu laifin da bindigu guda biyu kirar AK47, da kunshin harsashi, Adda, baburan hawa da kuma kakin soja.
Moshood ya ce "Masu laifin sun amsa laifukan da suka aikata daban-daban. Kuma hukuma tana cigaba da bincike domin kama ragowar da ake zargi, sannan nan bada jimawa ba za a mika su kotu domin shari'a".
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng