Kaki ba leda ba: Wani saurayi zai shafe wata 10 a garkame saboda yin Sojan gona

Kaki ba leda ba: Wani saurayi zai shafe wata 10 a garkame saboda yin Sojan gona

- Garin son fafa a matsayin Soja, idon wani matashi ya raina fata

- Bayan tursasa wani mutum ya karbe masa katin ATM sannan ya cire kudi da shi

- Akali ya yanke masa hukunci tare da sassauci kasancewar bai wahalar da kotu ba

Wata Kotu da ke Abuja ta daure wani matashi mai suna Joseph Ogar watanni 10 bisa laifin Sojan gona da kuma zamba cikin amincin da ya yiwa wani mai suna Godwin Ifraimu. Inda ya damfare shi kudi kimanin Naira 120,000.

Kaki ba leda ba: Wani saurayi zai shafe wata 10 a garkame saboda yin Sojan gona
Kaki ba leda ba: Wani saurayi zai shafe wata 10 a garkame saboda yin Sojan gona

Joseph Ogar wanda mazaunin kauyen Kuchikowa da ke yankin Nayanya a jihar Nasarawa, an same shi da aikata laifuffuka har guda biyu, wadanda su ka hadar da laifin Sojan gona da kuma sata

Tun da farko dai Alkalin kotun Maiwada Danjuma ya yanke wannan hukuncin ne, bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

KU KARANTA: ‘Yan Boko Haram sun ga ta kansu: Sojin saman kasar nan ta yi musu barin wuta (Bidiyo)

Mai shari’ar ya bukaci Joseph Ogar da ya biya kudi kimanin Naira 17,00 zabin tara sannan ya dawo da kudin da ya damfarar Godwin tare kuma da jan hankalinsa akan ya guji aikata irin wannan laifin.

A nata bangaren ‘yar sanda mai gabatar da kara ta bayyanawa kotun cewa a ranar 18 ga watan Yunin da ya gabata ne Joseph Ephraim wanda dan asalin kauyen Mabushi ne aka damke shi sakamakon yin Sojan gona a matsayin jami'in Soja.

"Ya karbi katin cire kudi na ATM mallakar Godwin Ifraimu tare da wayar tafi da gidanka kirar TECHNO CX wadda kudinta ya kai Naira 50,000, tare da tilasta masa bayyana lambar sirrinsa, ba tare da ya bayyanawa Ephraim laifin da ya aikata ba". Daga nan sai ya garzaya wani banki, inda ya cire kudi adadin Naira 120, 000.

T a bayyana cewa wannan ya saba da sashi na 321 da kuma sashi na 287 na kundin laifuka.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng