Wasu ‘Yan Majalisar dokokin jihar Kano na shirin yiwa Ganduje tutsu
- Barewa ba ta gudu danta yayi rarrafe, a cewar masu iya magana
- Wasu 'yan kwankwasiyya na halak malak daga cikin 'yan majalisar Kano na shirin binsa PDP
- Tun jiya dai ake raderadin cewa wasu sun fice amma majalisar ta karyata hakan
Bayan Kwana daya da ficewar tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso daga jamiyyar APC zuwa jamiyyar PDP, wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda 6 sun kudiri aniyar binsa zuwa jamiyyar PDP.
Rahotanni dai sun bayyana cewa wadanda ake tunanin za su bi Sanata Rabiu Kwankwaso sun hada da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, da na Gwale da kuma na Madobi, ragowar sun hada da na Gezawa, Gwarzo da kuma Rogo.
‘Yan Majalisun sun bayyana cewa har ‘yanzu lokaci bai yi ba, da za su yanke hukunci.
KU KARANTA: Bayan fitar Kwankwaso daga jamiyyar APC ko Gwamna Ganduje zai cire jar Hula (Rahoto)
Sai dai a wani labarin kuma majalisar dokokin ta jihar Kano ta musanta cewa wasu daga cikin mambobinta guda ashirin da biyu sun fice daga jam’iyyar APC zuwa Jam’iyar PDP.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Muhammed Bello Butu-Butu ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da yammacin jiya.
Ya ce mambobin majalisar musamman wadanda ke bangaren gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje su sama da talatin, ko mutum daya daga cikin su bai koma jam’iyyar PDP ba, kuma basa fatan hakan zai faru nan gaba.
Bello Butu-Butu wanda shine dan majalisa mai wakiltar mazabar Tofa da Rimin-Gado, ya ce ko da yake suna sane da wasu mutane shida a cikinsu da ke goyon bayan tsohon gwamnan Kano, amma har ya zuwa yanzu ba su sanar da su cewa sun sauya sheka zuwa PDP ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng