Tir: Gwamnatin jihar Kaduna ta gina wajen shakawata a gidan Hunkuyi da ta kwace

Tir: Gwamnatin jihar Kaduna ta gina wajen shakawata a gidan Hunkuyi da ta kwace

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara gina wajen wasan yara akan filin gidan Sanata Suleiman Othman Hunkuyi wanda ta rusa a baya kuma ta kwace dake lamba 11B titin Sambo, cikin unguwar Rimi ta jihar Kaduna.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito a watan Feburairun shekarar 2018 ne hukumar kula da filaye ta jihar Kaduna, KADGIS, ta rusa gidan Sanatan a dalilin karya dokokin gini da tace ta kama Sanatan dasu.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari ya yi ma babban Sufetan Yansanda gayyatar gaggawa

Tir: Gwamnatin jihar Kaduna ta gina wajen shakawata a gidan Hunkuyi da ta kwace

Gidan Hunkuyi

A lokacin da aka rushe wannan gida, Sanata Hunkuyi ya mayar da shi sakatariyar ofishin APC Tawariyya ta jihar Kaduna, wannan na daga cikin dalilan da suka sanya gwamnatin jihar Kaduna rushe gidan har kasa, wanda ake zargin gwamnan da kansa ne ya kaddamar da rushewar.

A wani ziyara da majiyar Legit.ng ta kai gidan a ranar Talata, ta tarar da leburori na ta aikin gini, da ta tuntubi Kaakakin hukumar kula da gine gine da tsara birane na jihar, KASUPD, Nuhu Garba, sai yace tabbatasa ana gina wajen wasan yara ne biyo bayan kwace filin.

“Idan zaka iya tunawa a lokacin da aka rushe gidan, an kwace mallakinsa, inda gwamnati ta mika shi ga hannunsu, don haka ne ya sa muke gina wajen wasan yara da wajen shakawata a yanzu.” Inji shi.

A kwana kwanan ne wata babbar Kotun jihar Kaduna ta fatattaki karar da Hunkuyi ya shigar gabanta domin ta kwato masa hakkinsa, inda a ranar 3 ga watan Yuli, Mai Shari Muhammad Lawa Bello ya yi fatali da bukatar Sanata saboda rashin inganci.

Tir: Gwamnatin jihar Kaduna ta gina wajen shakawata a gidan Hunkuyi da ta kwace

Gidan Hunkuyi

A bukatar da Hunkuyi ya mika ma Kotun ya bukaci ta haramta ma gwamnatin jihar Kaduna da hukumominta kwace masa fili duk da cewa suna zarginsa da kin biyan harajin kasa gida na shekaru aru aru, haka zalika ya nemi su biya shi naira biliyan goma kudin fansa.

Yayinda anata bangare, gwamnatin ta bayyana cewa tun asali an ware wannan fili ne saboda gina wajen shakatawa, amma Sanatan ya amsa ya gina gida akansa, wanda hakan ya bata taswirar jihar Kaduna, sai dai Hunkuyin bai hakura ba, inda ya daukaka kara.

Sai dai Hunkuyin ya bayyana cewa: “Wannan gini da gwamnati ke yi ya saba ma doka, sa’annan barazana ce ga Dimukradiyya da tsarin bin doka da ka’ida, wanda ya kamata duk mai hankali yayi Allah wadai da shi, idan an taa Hunkuyi yau, watakila kanka za’a sauka a gobe.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel