Babu hannun mu a harin da aka kaiwa gwamnan Filato a yankinmu – ‘Yan kabilar Berom

Babu hannun mu a harin da aka kaiwa gwamnan Filato a yankinmu – ‘Yan kabilar Berom

- A ranar Asabar da ta gabata ne mazauna sansanin ‘yan gudun hijira dake Jos, jihar Filato, suka kaiwa tawagar gwamnan jihar, Simon Lalong, hari

- ‘Yan kabilar Berom sun yi alla-wadai da harin da aka kaiwa Lalong tare da nesanta kansu da batun kai harin

- Sansanin ‘yan gudun hijrar na yankin da ‘yan kabilar Berom ne

Wasu fitattun kungiyoyin ‘yan kabilar Berom sun koka a kan yadda ake kokarin alakanta harin da aka kaiwa gwamnan jihar, Barista Simon Bako Lalon, da kabilanci.

A ranar Asabar da ta gabata ne mazauna sansanin ‘yan gudun hijira dake Jos, jihar Filato, suka kaiwa tawagar gwamnan Lalong hari. Sansanin ‘yan gudun hijrar na yankin‘yan kabilar Berom ne.

Babu hannun mu a harin da aka kaiwa gwamnan Filato a yankinmu – ‘Yan kabilar Berom
Simon Lalong

A jiya ne wasu manyan kungiyoyin ‘yan kabilar Berom guda biyu; Berom Youth Moulders Associatin da Berom Patriots suka fito suka shaidawa duniya cewar harin da aka kaiwa Lalong din bashi da nasaba da kabilanci saboda ya lamarin ya faru ne a wurin da kabilu da dama ke zaune.

DUBA WANNAN: An hangi Kwankwaso a Coci ranar juma'a ba jar hula

Danchollom Badung, shugaban wata kungiya ta ‘yan kabilar Berom mai suna “Berom Patriots” ya bayyana cewar batagarin da suka kai harin na son shafawa mutanensu bakin jinni wurin gwamnan saboda kasancewar inda lamarin ya faru, jama’arsu keda rinjayen jama’a.

Yawaitar samun hare-hare a Filato na cigaba da dusashe farinjin Lalong tare da zarginsa da kasa taka rawar gani wajen kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyi a jihar tasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng