Jagwalgwalo: Wani katon asara ya auri kanwar sa a jihar Anambara
Wani lamari mai cike da daure kai ya auku a jihar Anambara dake yankin kudu maso gabashin kasar nan inda muka samu labarin cewa wani malamin lissafi a makarantar sakandare a karamar hukumar Aguata mai suna Chiadikobi Ezeibekwe, ya auri kanwar sa ta jini.
Kamar dai yadda muka samu shine kanwar ta sa da ya aura tana da shekara 17 ne a duniya kuma Mista Chiadikobi Ezeibekwe ya bayyana cewa Allah ne ya kaddara zai auri kanwar ta sa inda ya kuma ce shi bai yi nadamar aikata hakan ba domin kuma ko a cikin addinin kiristanci ba bu inda aka haramta hakan.
KU KARANTA: Mafi yawan 'yan Boko Haram Kirista ne - Sabon rahoto
Legit.ng ta samu cewa sai dai daga baya mafusatan matasa a garin da lamarin ya auku sun tayar da tarzoma tare da kona cocin da aka daura auren.
A wani labari kuma, Wani gungun al'umma mabiya addinin kirista dake a yankin arewacin Najeriya karkashin inuwar kungiyar Kiristoci da kuma fastoci 'yan asalin arewacin Najeriya din watau Arewa Christians and Indigenous Pastors Association a turance sun yi kira ga daukacin al'ummar duniya da su taimaka su tsame su daga mulkin shugaba Buhari.
Wasu daga cikin manyan shugabanni da kuma hukumonin duniyar da kungiyar ta rubutawa takarda sun hada tarayyar Afirka, gamayyar kasashen turai da kuma kasashe renon Ingila.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng