Jami’an gwamnati sun tsere ta gatanga yayinda tsoffin yan bindiga suka yi zanga zanga a Ondo
Akalla tsoffin yan bindiga sama da 100 daga yankin Ese-Odo na jihar Ondo ne suka damke jami’ai a ofishin gwamna kn rashin biyansu alawus dinsu.
A lokacin zanga zangan, wasu jami’an gwamnati sun tsere ta hanyar haura Katanga sannan an damke sauran manyan jami’ai a ofishin gwamna, Alagbaka na tsawon sa’a’i da yawa.
Fusatattun masu zanga-zangan sun rufe komai na ofishin gwamnan, inda suke wakoki da zargin gwamnatin jihar da karbe masu bindigogi sannan ta ki basu tallafi.
Idon shaida sun bayyana cewa jami’an tsaro dake mashigin sun kasa yin komai yayinda masu zanga-zangan suka shige harabar sannan suka rufe mashigin. An yi barazanar harbin jami’an tsaron da suka turje.
KU KARANTA KUMA: Babu shaidar da ya nuna cewa anyi magudin zabe a Ekiti - CDD
Gwamna Rotimi Akeredolu baya a jihar domin ya raka shugaban ka Muhammadu Buhari karar Netherland.
Tsoffin yan bindigan sun zargi Rotimi da yaudararsu ta hanyar karbe makamansu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng