Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da N35.613bn don gina titina da kadoji

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da N35.613bn don gina titina da kadoji

- Gwamnatin Buhari zata gudanar da manyan aiyuka a kasar nan

- An amince da fitar da makudan kudaden ne yau Laraba a zaman majalisar zartarwa ta kasa

A yau larabar majalisar zartarwa ta amince da bayar da kwangilar gina wasu tituna da gadoji a fadin kasar nan.

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da N35.613bn don gina titina da kadoji
Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da N35.613bn don gina titina da kadoji

Ministan Makamashi, aiyuka da gidaje , Babatunde Fashola, ya bayyanawa manema labarai hakan jim kadan da kammala zaman wanda shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta.

Ya bayyana cewa an ware sama da Naira biliyan takwas domin gina gadar Ikom da kuma wani titi duk a birnin kalaba da ke jihar Cross River. Ya kara da cewa yin wannan aikin zai saukaka harkokin sufuri, sannan kuma aikin zai dauki tsawon watanni 24 ana gudanar da shi.

KU KARANTA: NNPC ta shiga chakwakiya: Majalisa zata binciki Naira N100b da ba’a saka a asusun gwamnati ba

Sannan kuma an ware sama da Naira biliyan N11b domin yin aikin titin a jihar Yobe tare kuma da ware sama da Naira biliyan N8b domin yin aikin titi a jihar Kwara.

Daga karshe ya kara da cewa an ware wasu kudin sama da naira biliyan N5b, domin yin aikin titi a jihar Abia tare kuma da ware Naira miliyan N933m domin samar da kayan aiki a babban kamfanin kula da makamashi na kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng