Chris Ngige yayi subutar-baki yayi kira a zabi su Fayose a zaben Ekiti

Chris Ngige yayi subutar-baki yayi kira a zabi su Fayose a zaben Ekiti

Mun samu labari cewa daya daga cikin Ministocin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi subul-da-baka ya nemi Jama’an Ekiti su zabi ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.

A wani bidiyo da ya shigo hannun mu an ga Ministan kwadagon kasar nan Sanata Chris Ngige ya nemi al’ummar Jihar Ekiti su zabi ‘Dan takarar Gwamna Ayo Fayose na Jam’iyyar PDP a zaben da za ayi a karshen wannan makon.

Chris Ngige yayi subutar-baki yayi kira a zabi su Fayose a zaben Ekiti
Ngige yayi wa Gwamna Ayo Fayose kamfe a Jihar Ekiti

Ministan ya bayyana cewa an yafewa Mutanen Jihar Ekiti da su ka zabi Ayodele Fayose a zaben 2014 lokacin Goodluck Jonathan sai dai kuma yayi subutar baki ya nemi Mutanen na Ekiti su marawa Fayose baya a zaben Ranar Asabar dinnan.

KU KARANTA:Fayose na kokarin hana Shugaban kasa Buhari zuwa kamfe

Chris Ngige yayi nufin yace jama’a su zabi Kayode Fayemi ne sai kurum yayi kuskure yace a zabi Ayo Fayose. An dai yi kokarin a jawo hankalin Ministan na Shugaba Buhari sai dai tuni ya furta hakan a lokacin da yake jawabi wajen kamfe dazu.

Sanata Ngige dai ya nuna cewa idan har mutum ya auri mata 2 zai fi sanin wanda ta fi don haka yace yanzu al’umar Ekiti sun gane na zaba tsakanin su Ayo Fayose. A karshen makon nan ne za a kara tsakanin Kola Olobodiyan da Kayode Fayemi.

Dazu kun ji cewa Ministan Ma’adanai na kasa Dr. Kayode Fayemi wanda ya fito takarar Gwamnan Jihar Ekiti a Jam'iyyar APC yana cigaba da kamfe. Kayode Fayemi wanda tsohon Gwamnan Ekiti ne ya rabawa al’umma fetur kyauta jiya domin su zabe sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel