Nigerian news All categories All tags
Asirin wata mai siyar da abinci ya tonu bayan ta damfari wani maras lafiya 400,000 wai za tayi masa magani

Asirin wata mai siyar da abinci ya tonu bayan ta damfari wani maras lafiya 400,000 wai za tayi masa magani

- Karshen damfarar wata likitar bogi yazo, bayan da asirinta ya tonu

- Sana'ar sayar da kayan abinci take amma kuma a hakan take fakewa da sunan ma'aikaciyar jiyya

Jami'an tsaro sun cafke wata Mata mai suna Mercy Duru Ezinne, ƴar kimanin shekaru 35 a Duniya da ta ke sojan Gona a matsayin Likita.

Asirin wata mai siyar da abinci ya tonu bayan ta damfari wani maras lafiya 400,000 wai za tayi masa magani

Asirin wata mai siyar da abinci ya tonu bayan ta damfari wani maras lafiya 400,000 wai za tayi masa magani

Tun da farko dai wani mai tireda ne ya tuntube ta akan wani marar Lafiya, mai suna Hassan Olawale, wacce ta gaya musu ai ciwon ne ke damunsa, kuma ta nuna Tabbas sai an yi masa dashen koda.

Hassan Olawale ya shiga cikin mawuyacin hali ne biyo bayan maganin da likitar bogin ta bashi bisa larurar da ta ke damunsa, in da yake karbar magani a wani asibiti mai zaman kansa dake yankin Ibara a cikin garin Abeokuta.

KU KARANTA: Yansanda: Mun tabbatar da kashe magajin gari a jihar Zamfara da 'yan bindiga suka yi

Kafin ta ba shi maganin sai da ta karbi kudi kimanin naira 400,000 daga hannun majinyacin.

Da ta ke wa jami'an tsaro bayani ta bayyana cewa, ita ba likita ba ce amma na samu horo na musamman akan aikin jinya, kuma yanzu haka ina sana'ar sayar da kayan abinci ne.

Mutane suna daukata a matsayin likita, sabo da ganin yadda alakata take da likitoci wadanda su ke abokai na ne. Kuma Ina yawan zuwa asibiti gurin likitocin abokai na, domin ganin yadda zan cigaba da karatu na.

"Kimanin mako uku ke nan da su ka wuce, wani makocina ya gabatar da wani majiyanci mai suna Hassan Olawale, wanda ni Kuma na tura shi zuwa dakin gwaje-gwaje domin gano cutar da ke damunsa, inda aka gano yana fama da cutar koda ne" in ji likitar bogi Mercy.

In da shi kuma nan take ya kirawo likitansa mai suna Raji, shi kuma ya tabbatar masa ba shi da bukatar a yi masa dashen koda, amma yana bukatar a dora shi akan na'ura ta musamman da zata tallafi rayuwarsa. Wanda sai ya biya kudi kimanin naira miliyan 10.

Jin wannan lafazin likitan ne ya sa na bukaci ya kawo wadannan kudaden domin na kawo masa wasu magunguna da zai yi amfani da su. In ji Mercy.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel