Jakadan Najeriya a Saudiyya ya musanta zargin daukar ma’aikata a boye

Jakadan Najeriya a Saudiyya ya musanta zargin daukar ma’aikata a boye

Jakadan Najeriya a Saudiyya, Isa Dodo, ya karyata zargin da wasu ke yi na cewa da hadin bakin sa ake safarar mata daga Najeriya ana kai su Saudiyya su na yin aikatau.

A wata hira da kamfani dillacin Labaran Najeriya, NAN ta yi da shi a ranar Laraba, Dodo ya ce babu kamshin gaskiya a zargin.

Ya ce babu ruwan Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya da shi kansa da ofishin sa a lamarin fitar mata masu aikatau zuwa Saudiyya.

Jakadan Najeriya a Saudiyya ya musanta zargin daukar ma’aikata a boye
Jakadan Najeriya a Saudiyya ya musanta zargin daukar ma’aikata a boye

Ya ce masu yin wannan sana’a su na yi ne ba tare da sanin Ma’aikatar Harkokin Waje a Abuja ba, ko kuma ofishin sa da ke Riyad, kasar Saudiyya.

KU KARANTA KUMA: Kalli kayatattun hotuna daga Kamun auran ‘ya’yan Indimi Hauwa da Meram wanda aka yi a Maiduguri

Yayin da ya ke jan hankalin jama’a, ya kara da cewa an ce tun sama da shekara uku ake wannan safarar mata, to amma shi watan sa bakwai kawai da kama aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng