Buhari: Ni ba barawo bane, kuma babu wanda ya isa yace na saci wani abu a kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace masu kalubalantar shi akan yanda yake tafiyar da mulki a kasar baza su iya cewa shi barawo bane, sannan kuma babu wanda ya isa yace yana satar kudin talakawa a kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace masu kalubalantar shi akan yanda yake tafiyar da mulki a kasar baza su iya cewa shi barawo bane, sannan kuma babu wanda ya isa yace yana satar kudin talakawa a kasar nan.
Shugaba Buhari yace baya dana sani akan kasancewar shi mutum mai gaskiya da nagarta.
Kamar yanda mai magana da yawun shi, Garba Shehu, ya fada a fadar shugaban kasar a Abuja jiya, yayin bada masauki ga wakilan shari'ar koli ta Najeriya.
DUBA WANNAN: Gobara mai karfi ta cinye wani yanki na jihar California dake kasar Amurka
Shugaban kasan yace yana farin cikin hana kanshi da na kusa da shi kwangiloli.
Yace bai bada kwangila ko daya ga wadanda ya sani ba, sannan kuma shi bai ma damu da wanda yayi ba matukar anyi aiki mai kyau kuma a farashin da ya dace.
Shugaba Buhari yace da ya saci rijiyar man fetur a lokacin da yake ministan man fetur, to da yayi gidan yari.
"Na zabi ministoci na, kuma suna aiki. Ina kuma daraja nagartar su. A lokacin da suka zo nan, (Federal Executive Council Chambers), mun tabbatar sunyi abinda ya dace. Idan da na mallaki rijiyar man fetur, da naje gidan yari," inji Buhari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ma bakin shi yana cikin mawuyacin hali akan zaben masu taya shi aiki.
Mai magana da yawun wakilan da suka ziyarci shugaban kasan, Sheikh Hadiyyatullahi Abdulrashid, ya yabawa shugaba Buhari inda yace ya cika alkawurran da yayi lokacin zabe.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng