Gwamnatin tarayya ta shirya hanyoyi 6 da zata magance rikicin makiyaya da manoma

Gwamnatin tarayya ta shirya hanyoyi 6 da zata magance rikicin makiyaya da manoma

Gwamnatin tarayya ta gabatar da wani shiri na magance rikicin makiyaya da manoma a kasar, wanda yayi sanadiyan mutuwar dubban mutane tsawon shekaru da dama.

An kashe daruruwan mutane a 2018 kadai a rikicin na makiyaya da manoma a jihohi kamar su Benue, Plateau da Kaduna.

Mataimakin shugaban kungiyar tattalin arzikin kasa, Andrew Kwasari ne ya gabatar da shirin a jiya a Abuja.

Muhawaran Kwasari ya nuna cewa shirin ya kasance ne daga tarurruka da shawarwari da ma’aikatar gona da raya karkara da kuma na kungiyar tattalin arzikin kasa a 2017.

Gwamnatin tarayya ta shirya hanyoyi 6 da zata magance rikicin makiyaya da manoma
Gwamnatin tarayya ta shirya hanyoyi 6 da zata magance rikicin makiyaya da manoma

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar kungiyar tattalin arzikin sannan akwai gwamnonin jihohi gaba daya da wasu ministoci a ciki.

KU KARANTA KUMA: Ka daina tafiye-tafiye marasa amfani – Sarki ga gwamnan jihar Zamfara

Wadannan hanyoyi shida da gwamnatin zata bi sune:

1. Zuba jarin tattalin arziki ta yadda Gwamnati zata bayar isasshen tallafi da zai bunkasa harkar nomad a kiwo a jihohin da wannan rikici ke faruwa.

2. Sasanta rikici da kuma yin abubuwan da zai sa aminci a tsakanin bangarorin biyu

3. Aiki da doka domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu

4. Bayar da tallafi na Kayayyakin agaji ga wadanda abun ya shafa kamar gyaren gidaje da wuraren bauta da aka lalata

5. wayar da kai tare da karama juna sani kan abubuwan da wannan rikici ka iya haifarwa kamar asarar dukiyoyi da lalata makarantu.

6. Tattauna lamuran da suka shafi bangarorin biyu domin samun mafita.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel