Dogo-zauren-yunwa: Ku sadu da saurayi dan shekara 15 da ya fi dukkan sa'annin sa tsawo a Najeriya

Dogo-zauren-yunwa: Ku sadu da saurayi dan shekara 15 da ya fi dukkan sa'annin sa tsawo a Najeriya

Hoton wani matashi dan Najeriya daga jihar Imo da ya fita a kafafen sadarwar zamani ya baza rudu da cece-kuce musamman ma ganin yadda tsawon sa ya bar kowa cikin al'ajabi.

Matashin dai mai suna Fortune Ibe an ce shekarun sa 15 a duniya amma tsawon sa ya kai ma'aunin tsawo na kafa 6 da inci 9 da digo 5 wanda hakan ne ma ya sa ake tunanin yafi dukkan sa'annin sa tsawo a Najeriya.

Dogo-zauren-yunwa: Ku sadu da saurayi dan shekara 15 da ya fi dukkan sa'annin sa tsawo a Najeriya
Dogo-zauren-yunwa: Ku sadu da saurayi dan shekara 15 da ya fi dukkan sa'annin sa tsawo a Najeriya

KU KARANTA: Sharudda 4 da su Kwankwaso suka bayar na zaman su APC

Legit.ng ta samu cewa matashin ya ce a duk shekara yana kara tsawo da akalla inci 5 kuma yace yana sha'awar ya rika buga wasan kwallon kwando.

Yanzu dai matashin ya samu gurbin karatun jarida a jami'ar Covenant bayan kammala karatun sa na Sakandare.

Matashin dai ya bayyana cewa yakan ja wa kansa kallo a duk inda yaje musamman ma idan ya fadi shekarun sa inda a lokuta da dama mutane kan musanta adadin shekarun nasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel