Daukar ma’aikata: Hukumar yan sanda ta saki sunayen mutane 5,253 da suka yi nasara a fadin kasar
Hukumar yan sandan Najeriya ta yi gayyaci mutanen da suka yi nasarar cin jarabawar daukar aiki da ta gudanar a ranar Juma’a da su zo a duba lafiyarsu.
Bisa ga sunayen da aka wallafa a shafin yanar gizon rundunar yan sandan, https://psc.org.ng/candidateslist/, an umurci wadanda suka yi nasara da su je a tattance su a hedkwatan hukumar yan sanda na jihohinsu tsakanin ranar 31 ga watan Mayu da 3 ga watan Yuni.
Daga cikin mutane 37,000 da suka rubuta jarrabawar, 5, 107 suka yi nasarar shiga jerin wadanda za’a tattance a hukumar lafiyar kamar yadda majiyarmu ta Premium Times ta ruwaito.
Daga cikin mutanen 5,253 jihar Kano ce keda mafi yawan mutane da suka kai 308 inda Katsina ke bin ta da mutane 238.
Jihar Oyo na da mutane 225 inda ta zamo na uku, sannan Akwa Ibom na da mutane 194 yayinda aka zabi 189 daga jihar Borno. Jihar Jigawa na da mutane 189.
Hakazalika jihar Abia na da 114, Adamawa 140, Anambra,146 .Bauchi,133, Benue 157, Cross River 122, Delta 166, Ebonyi 91, Edo 125, Enugu 119, Imo 181, Kaduna 161, Kebbi 144, Kogi 140, Kwara 110, Lagos 136, Niger kuma na da 169.
A jihar Ogun mutane 140 candidates ne suka samu shiga matakin, Ondo na da125, Osun 211, Plateau 116, Rivers 138, Sokoto 161.
KU KARANTA KUMA: Kama Lamaran Yero: Da ana bin ta laifi ne da Buhari ma bai zama shugaban kasa ba - Sheikh Gumi
Taraba na da 112. Yobe na da 110 sannan kuma Zamfara na da 99.
Wasu jihohin mutane kalilan ne suka samu shiga inda suka hada da babban birnin tarayya 42, Bayelsa 54, Gombe 75 sannan Ekiti 84.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng