Duk da matsalar tattalin arziki a Najeriya, munyi aiki fiye da yanda ake tunani - Gwamnatin Tarayya

Duk da matsalar tattalin arziki a Najeriya, munyi aiki fiye da yanda ake tunani - Gwamnatin Tarayya

A jiya ne gwanatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo gagarumin cigaba a cikin shekaru uku da tayi akan mulki

Duk da matsalar tattalin arziki a Najeriya, munyi aiki fiye da yanda ake tunani - Gwamnatin Tarayya
Duk da matsalar tattalin arziki a Najeriya, munyi aiki fiye da yanda ake tunani - Gwamnatin Tarayya

A jiya ne gwanatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo gagarumin cigaba a cikin shekaru uku da tayi akan mulki.

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed shine ya fadi hakan a wani taron manema labarai da akayi a jihar Legas, wanda akayi akan shekaru uku da shugaba Buhari yayi akan mulki.

Ministan yace cikin shekaru ukun Najeriya tana farfadowa "Kamar konannen gidan da ake mashi sabon gini, bayan shekarun da aka dauka ana wawure kudin kasar, rashin shugabanci na gari da kuma faduwar kudin danyen mai a duniya."

DUBA WANNAN: Rikicin Jam'iyyar APC: Za'ayi zaman karshe tsakanin sabuwar jam'iyyar nPDP, shugaba Buhari da Osinbajo a yau

Kamar yanda yace, yayin da 'yan adawa ke nuna basu yi komai ba a shekaru ukun da suka yi, da dama daga cikin 'yan kasar suna jinjiinawa kokarin da gwamnatin take yi.

"Tayi abubuwa da yawa, duk da matsalar da kasar ke ciki na karyewar tattalin arziki. "

Ya cigaba da cewa tun a watan Mayun shekarar 2015 da shugaba Buhari ya haye kan kujerar mulkin kasar, 'yan ta'addar Boko Haram sun mamaye kananan hukumomi 24 a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

"A yau, mun samun nasara a bangarori uku: Bangaren tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Rana bata karya kamar yanda mutane ke fada."

Ya bayyana cewa karfin samar da wutar lantarki ya kai 7,000mw daga 2,690mw da suka samu a shekarar 2015. Za a kuma samu karin 2,000mw nan da karshen shekara.

Ministan yace gwamnatin ta farfado da ababen more rayuwa a kasar nan, irinsu wutar lantarki, tituna da hanyoyin jirgin kasa da naira tiriliyan 2.7 kacal.

Idan zamu iya tunawa, a 2014, gwamnatin tarayya ta kashe Naira biliyan 154 akan ababen more rayuwa, wanda ya hada da sufuri (Naira biliyan 14), Noma da ruwan sha (Naira biliyan 34), wutar lantarki, aiyuka da gidaje (Naira biliyan 106).

Ministan yace darajar Naira ta fadi a watanni 15 da suka wuce, daga kashi 18.7 a cikin dari zuwa kashi 12.5 a cikin dari a watan Afirilu 2018, ma'ajiyar kasar na da dala biliyan 48, mafi yawa a shekaru 5 da kuma fiye da rubanya dala biliyan 23 da Gwamnatin ta tarar a 2015.

Ya cigaba da bayyana cigaban da aka samu sun hada da social intervention programme (SIP) wanda a karkashin shi ana ciyar da mutane 3,000,000 wadanda basu da karfi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel