Garabasa: Wani mai adai-daita sahu a Kano yana daukar mutane kyauta albarkacin watan Ramadana
A wani yunkuri na neman rahamar ubangijin sa, wani matashi mai sana'ar adaidaita Sahu ko Keke Napep a garin Kano ya shelanta garabasar daukar mutane kyauta albarkacin shigowar watan azumin Ramadana.
KU KARANTA: Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta ga 'yan Boko Haram
Matashin mai suna Umar Saidu dai an ganshi ne da takardar makale a bayan adai-daita sashun nashi dauke da rubutun da ke nuni da bayanin da muka bayar a sama a cikin harshen turanci.
Legit.ng ta samu cewa hoton sa din dai ya dauki hankalin jama'a sosai a shafukan sadarwar zamani dukkan fadin kasar nan musamman ma a tsakanin musulmai wadanda suka gode masa tare da sa masa albarkar.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa an fara azumin watan Ramadana a kasashe da dama a fadin duniya ne a ranar Alhamis din da tagata ciki kuwa hadda kasar Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng