Adadin mutanen Najeriya zai karu da miliyan 189 daga 2018 zuwa 2050 - UN

Adadin mutanen Najeriya zai karu da miliyan 189 daga 2018 zuwa 2050 - UN

A wani rahoton majalisar dinkin duniya ta fitar mai suna: Revision of World Urbanisation Prospects, ya nuna cewa za'a samu kusan karin mutane kusan Biliyan 2.5 wadanda zasu koma rayuwa a birane nan da shekarar 2050

Adadin mutanen Najeriya zai karu da miliyan 189 daga 2018 zuwa 2050 - UN
Adadin mutanen Najeriya zai karu da miliyan 189 daga 2018 zuwa 2050 - UN

A wani rahoton majalisar dinkin duniya ta fitar mai suna: Revision of World Urbanisation Prospects, ya nuna cewa za'a samu kusan karin mutane kusan Biliyan 2.5 wadanda zasu koma rayuwa a birane nan da shekarar 2050.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa a rahoton da Fannin tattalin arziki da walwalar jama'a (DESA) ya fitar ya nuna cewa "Nan da shekarar 2050, Najeriya zata zama kasa ta uku a duniya mafi yawan al'umma, wacce a yanzu take akan mataki na bakwai, inda zata maye gurbin kasar Amurka."

DUBA WANNAN: Wasu Yahudawa mazauna Ingila sunyi Allah wadai ga kasar Isra'ila

DESA tace komawar mutane zuwa biranen zai faru ne cikin kankanin lokaci.

"Hasashen ya nuna cewar kasar India, China da Najeriya su zasu samu kashi 35 a cikin dari na hau hawan mutanen da ke komawa birane a tsakanin 2018 da 2050.

"Rahoton ya nuna cewa kasar India zata samu karuwar mutane mazauna birane kusan miliyan 416, China kuma miliyan 255 da Najeriya mai miliyan 189" a rahoton DESA.

Sashin majalisar dinkin duniyan yace nan da 2050, cikin kashi biyu a cikin duk kason mutane uku dake rayuwa a kauye zasu koma birane, don haka ne bukatar tsarawa da inganta rayuwar birane ta taso.

Wannan rahoton ya nuna cewa gurin mutane biliyan 2.5 zasu koma rayuwa a birane a tsakiyar karnin nan, a hasashen da DESA ta fitar.

Rahoton ya kara da cewa, duniya zata samu karin manyan birane 43, daga cikin 31 da ake dasu yanzu.

Manyan birane sune biranen da ke da mazauna sama da miliyan 10 kuma rahoton yace yawancin manyan biranen akan samesu ne a kasashe da ke tasowa.

Anyi hasashen cewa nan da 2028, babban birnin India, New Delhi, zai zama babban birnin da yafi yawan jama'a a duniya.

A halin yanzu, Tokyo ce babban birnin a duniya, mai mutane miliyan 37, New Delhi ke binta da mazauna miliyan 29 da kuma Shanghai mai mazauna miliyan 26. Sai kuma Mexico city da Sao Paulo suke biye dasu da mazauna miliyan 22.

"Kasashe da yawa zasu fuskanci matsalolin da suka kunshi gidaje, sufuri, wutar lantarki da sauran abubuwan more rayuwa irinsu aikin yi, ilimi da cibiyoyin kiwon lafiya."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng