Ta shiga haukan da gan-gan don kada ta biya kudin mota
Wani direban tasi ya rasa hakkinsa bayan fasinjar da ya dauko ta rikide wai ita mahaukaciya ce kawai don ta ki biyansa hakkinsa.
Direban tasi din mai suna Attah, ya ce matar ta shigar motar sa ne kuma ta bukaci ya kai ta wani gidan rediyo da ke Kokolemle a kasar Ghana.
Bayan sun isa inda za ta sauka, matar da ce ma direban ya jira ta karbo masa kudinsa daga hannun wani a cikin gidan rediyon Hitz Fm.
KU KARANTA: Farfesa Sagay ya kare Sufeta Idris, ya ce Sanatocin Najeriya ne makiyan demokradiyya
Amma abin mamaki sai matar ta fara sauya yanayin ta tana babaudewa kamar wadda ke fama da ciwon hauka.
Hakan yasa Attah ya ciro tsumangiya daga cikin motarsa domin ya dandana mata kudar ta amma sai wasu ma'aikatan gidan rediyon da ke kallon abinda ke faruwa suka shiga tsakani lamarin ya tabarbare.
Direban tasi din ya yi kira ga sauran abokan aikinsa su sanya ido sosai kafin daukan fasinja don kaucewa fadawa halin da ya fada.
A wata rahoton kuma, Legit.ng ta ruwaito muku cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai gina wata katafaren asibitin zamani a garin Abuja tare da hadin gwiwa da wasu kwararu daga kasar Saudiyya da Jamus.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng