An ja kunnen gwamnati game da shigo da amfanin gona da aka sarrafa su da ilimin kimiyya
Wata kungiya mai zaman kanta ta gargadi gwamnatin tarayya game da shigo da kaya amfanin gona da ake sarrafa su da kimiyya da fasaha a dakunan gwaje gwaje zuwa kasuwannin Najeriya.
Premium Times ta ruwaito a shekarar 2015 ne gwamatin Najeriya ta rattafa hannu kan wani kuduri da ake yi ma kira da ‘Biosafety’ wanda zai shigar da Najeriya sawun kasashe masu amfani da kayan gona da aka sarrafa su a dakunan gwaje gwaje ta hanyar ilimin kimiyya.
KU KARANTA: Hare haren Yan bindiga: Sanata Shehu Sani ya zargi El-Rufai da daukan nauyin yan bindiga a Jihar
A yanzu haka gwamnati na gab da fara halasta shigo da auduga da waken suya da aka sarrafa su ta wannan hanya, kamar yadda shugaban hukumar kula da ire iren amfanin gonan, Rose Gidadi ta tabbatar.
Sai dai kungiyar dake zaman kanta, Mother Earth Foundation ta soki lamarin ta bakin shugabanta, Joyce Ebebinwe a ranar Alhamis 12 ga watan AFrilu, inda tace babu tabbacin amfanin gonan basu da dauke da wasu sinadarai da ka iya cutar da dan Adam.
Kungiyar ta cigaba da fadin akwai matsaloli da dama dake tattare da ire iren kayan gonan nan, da suka hada da guba, karya garkuwa jiki, sauya sindaran halitta da sauransu matsaloli, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Daga karshe kungiyar ta shawarci gwamnati ta inganta harkar noma kamar yadda aka santa, ta hanyar samar ma manoma taki, iri mai kyau da magunguna kwari, gina hanyoyi zuwa kauyuka, horas da manoma kan hanyoyin noma na zamani, kayan aikin noma, gonakai da bashi mai karancin ruwa da sauransu, inda suka ce hakan ne kadai zai inganta noma a Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng