Za a kafa wata katuwar Makarantar Sojojin Najeriya a Jihar Borno

Za a kafa wata katuwar Makarantar Sojojin Najeriya a Jihar Borno

- Za a kafa wata babbar Jami’a ta Sojoji a Arewacin Najeriya

- A jiya aka amince da wannan batu da aka dade ana magana

- Za a gina Makarantar ne dai a Garin Biu cikin Jihar Borno

A wannan makon ne Gwamnatin Tarayya ta amince da a kafa katuwar Makaranta ta Jami’a ta musamman ta Soji a Najeriya a Jihar Borno kamar yadda labari ya iso mana jiya da rana.

Za a kafa wata katuwar Makarantar Sojojin Najeriya a Jihar Borno
Gwamnatin Buhari ta amince a gina Jami’ar Sojoji a Borno

A taron Majalisa zartawa na NEC, Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya ja ragamar zaman na jiya a dalilin tafiyar da Shugaba Buhari yayi ya amince da a fara aikin gina Jami’ar Sojoji a Garin Biu a Borno.

KU KARANTA: Wasu mutane 10 sun sheka barzahu a Jihar Benuwe

Ministan ilmi na kasar Adamu Adamu ya bayyana wannan ga manema labarai bayan taron Majalisar inda ya tabbatar da cewa za a kara darajar wata Makaranta a Yankin zuwa Jami’ar Sojoji domin inganta ilmin tsaro a Najeriya.

Shugaban Hafsun Soja Janar Tukur Buratai ya kai Jami’ar Sojojin zuwa Garin su watau Biu da ke cikin Kudancin Jihar Borno. Mutanen Yanin Borno dai sun yi farin ciki da su ka ji Gwamnatin Buhari ta amince a gina Jami’ar Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng