Kano ce kadai Jihar Arewa da ke cikin manyan masu kudin shiga a bara

Kano ce kadai Jihar Arewa da ke cikin manyan masu kudin shiga a bara

Za ku ji Jihohin kasar nan da su ka fi kowa samun kudin shiga a shekarar 2017 kamar yadda Alkaluman BudgIT su ka nuna. Kowace Jiha dai na kokarin tatso kudi daga aljihun masu zama a Jihar domin yin ayyukan more rayuwa.

Ga Jihohin nan a jere kamar yadda za ku gani:

Kano ce kadai Jihar Arewa da ke cikin manyan masu kudin shiga a bara
Gwamna Ambode ya samu sama da Biliyan 300 a bara

1. Jihar Legas

Jihar Legas ce gaba da babban rara tun ba yau ba a Najeriya saboda yawan kamfanoni. A 2017 sai da Jihar Legas ta samu kudin shiga na Naira Biliyan 333.

KU KARANTA: CBN ta gargadi Shugaban kasa Buhari ya bi a hankali da kashe kudi

2. Jihar Ribas

Bayan Legas kuma sai Jihar Ribas mai arzikin man fetur a Neja Delta inda a bara kurum Gwamna Nyesom Wike na Jihar ya samu kusan Naira Biliyan 90.

3. Jihar Ogun

Makwabciyar Legas watau Ogun na cikin sahun gaba a wajen tatsar kudin shiga a Najeriya. A Jihar Ogun an samu kusan Naira Biliyan 75 a shekaran bara.

4. Jihar Delta

Ta hudu a jerin kamar yadda alkaluma su ka nuna ita ce Jihar Delta inda a shekaran da ta ta wuce ta tara abin da ya haura Biliyan 50 daga haraji da sauran su.

5. Jihar Kano

Idan ku ka lura dai duka Jihohin da aka ambata na Kudancin Najeriya ne in ban da Jihar Kano. Gwamatin Ganduje ta samu sama da Naira Biliyan 40 a bara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng